✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matar mawaki Davido ta haifi tagwaye

An yi haihuwar ce a kasar Amurka

Matar fitaccen mawakin nan na Kudancin Najeriya, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, wato Chioma Rowland, ta haifa masa tagwaye a kasar Amurka.

A cikin wani bidiyo da Oluwafifunmi Omodele ta wallafa a dandalin X, wanda aka fi sani ta Twitter a da, an ga Davido da Chioma suna fitowa daga asibitin da aka yi haihuwar.

Idan za a iya tunawa, a bara dan mawakin mai suna Ifeanyi, ya mutu ta hanyar nitsewa a cikin ruwa a gidan shi da ke unguwar masu hannu da shuni ta Banana Island da ke Legas.

Ya nitse ne bayan ya dafa wani kududdufin ninkaya, inda daga bisani aka garzaya da shi asibiti, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Tun a farkon makon nan ne dai labarin haihuwar ya baza gari, inda mutane da dama suka rika taya mawakin da matar tashi murna.