✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe iyayensa da tabarya

Babu wata sabani takaninsu, amma ya hallaka iyayensa

Wani matashi mai shekara 46 ya yi kashe iyayensa biyu ta hanyar amfani da tabarya.

Aminiya ta samu karin bayani game da wannan lamarin da ya faru a garin Aroji Mparagwu, yankin Nsukka Karamar Hukumar Igbo-Eze ta Kudu da ke Jihar Enugu a karshen makon da ya gabata.

Matashin wanda yake gudanar da harkokin kasuwancinsa a daya daga cikin Jihohin Arewa ya zo gida ne da nufin yin hutun bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara.

A ranar da zai kashe iyayen nasa, ya fara samun mahaifiyarsa ce, tana daka a turmi a dakin dafa abinci daidai da lokacin da kowace mace ke kokarin yin girkin abin da za a ci.

Yana shigowa dakin dafa abincin sai ya fisge tabaryar a hannun mahaifiyar tasa ya kwada mata a kanta ta fadi sumammiya, aka kwashe ta zuwa asibiti kafin a je ta mutu.

A lokacin da ya buge mahaifiyar da tabarya, yana fitowa daga dakin dafa abincin sai ya afka wa mahaifinsa mai suna Julius, shi ma ya kwada masa tabaryar a mukamikinsa.

Nan take ko shurawa mahaifin nasa bai yi ba, sai shi Micheal ya yi amfani da wayar tarho ta mahaifiyarsa da ya kashe ya rika kiran kannensa ta waya da ke Abuja da Legas yana cewa, mahaifiyarsu ba ta da lafiya, an kai ta asibiti.

Aminiya ta tuntubi daya daga cikin makwabtan Micheal da ya kashe iyayen nasa, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Ya ce: “Haka kawai babu wata matsala tsakaninsa da jama’a ko iyayensa, mu ma abin ya ba mu mamaki, ya bakanta mana rai.”

An sanar wa ofishin ’yan sanda da ke Ibagwa-Aka a Karamar Hukumar Igbo-Eze ta Kudu, nan take aka turo jami’an ’yan sanda suka kama shi kafin ya tsere.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Enugu, ASP Daniel Ndukwe ya tabbatar wa Aminiya afkuwar hakan.

Ya ce wanda ake zargi na hannunsu ana masa tambayoyi, da zarar an kammala kotu za a mika shi.