✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kashe mahaifinsa da tabarya a Jos

Babu zato, babu tsammani ya dauko tabarya ya buga wa mahafin a kai.

’Yan sanda sun damke wani matashi dan shekara 29 wanda ake zargin ya kashe mahaifinsa da tabarya a unguwar Kambel da ke Anglo-Jos a Jihar Filato.

Kwamishinan ’yan sandan jihar, Hassan Steve Yabanet, ya ce lamarin ya faru ne a lokacin da mahaifin ya samu sabanin da dan, wanda ba zato, ba tsammani ya dauko tabarya ya buga wa mahafin a kai.

Ya bayyana cewa wani makwabci ne ya kai rahoto a caji ofis da ke yankin Anglo-Jos a ranar 20 ga Fabrairu, bayan mahain ya rasu a Asibitin Kwararru na Jihar Filato inda yake jinya.

Kwamishinan ya ce an kama wanda ake zargin kuma bayan kammala bincike za a gurfanar da shi a gaban kotu.

Gawar kuma a cewarsa an kai ta dakin ajiyar gawarwaki na asibitin.