✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matashi ya kera motar ‘A kori kura’ a Yobe

Ya nemi a tallafa masa ya bunkasa fasahar

Wani matashi mazaunin garin Potiskum a Jihar Yobe ya kera mota samfurin ‘A kori kura’ mai daukar kaya domin saukaka jigilar amfanin gona.

Da yake zantawa da Aminiya a Potiskum, matashin, wanda manomi ne mai suna Mohammed Abubakar Mamuda ya kera ta ne domin ta taimaka wa sana’arsa ta noma.

A cewarsa, “Yanayi ne ya tilasta min yin bincike don samun mafita, ni manomi ne wanda ba ya iya sayen motar daukar taki zuwa gona da kuma tattara amfanin gona bayan girbi cikin sauki.

“Hakan ya sa na samu injinan babur mai kafa uku da wasu karafa daban-daban masu girma da kauri da sauran kayayyaki. Na aro na’urar walda daga wajen abokina kuma na kwashe watanni 8 ina kerawa.

“Motar tana da karfi, tare da ingantattun karafa masu nauyin gaske, kuma tana iya tafiya sosai kuma ko a yanzu na fara amfani da ita wajen kai takin gida da makamantan haka zuwa gona.”

Don haka ya  yi kira ga Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni, da Ma’aikatar Bunkasa Tattalin Arziki da Samar da Aikin yi da sauran masu ruwa da tsaki da su hada kai da shi wajen inganta wannan fasahar domin samar da karin masana’antu domin amfanin al’umma.

“Ni mai takardar shedar kimiyyar kwamfuta ne kuma na yi difloma a fannin kula da lafiya. Ina da sha’awar kera motoci, amma saboda kaddara, na kasa yin nazarin hakan.”

Mamuda ya yi fatan kai motar ga Gwamna Mai Mala Buni domin bajekolinsa da kaddamar da wasu masu hazaka domin su samu ci gaba.