✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matashin da ake zargi da yi wa mai shekaru 54 fyade ya shiga hannu

Kotun ta ba da belinsa a kan naira dubu dari biyar.

’Yan sanda sun gurfanar da wani matashi mai shekaru 27 a gaban kotu, bisa zarginsa da yi wa wata dattijuwa mai shekaru 54 fyade a gidanta.

Matashin ya bayyana a gaban kotun majistare da ke jihar Legas ne bisa zarginsa da aikata laifin yunkurin aikata fyade da cin zarafi.

Dan sanda mai gabatar da kara, Sufeta Courage Ekhuerohan ya bayyana wa kotun cewa wanda ake zargin ya aikata laifin ne ranar 11 ga watan Oktoba da misalin karfe 2:40 a kauyen Gemes da ke jihar.

Ya ce mutumin ya haura gidan matar ne ta taga, da niyyar yi mata fyade, sai dai ihunta ya sanya makwabta suka shigo kafin ya tsere, inda suka mika shi ga ’yan sanda.

Laifin dai ya sabawa sashi na 262, da na 263, da na 350, na kundin manyan laifukan jihar na 2015.

Alkaliyar kotun, Misis M.I Dan-Oni ta ba da belinsa kan Naira 500,000 ta kuma nemi ya gabatar da mutum biyuda za su tsaya masa kuma sun mallaki makamancin wannan kudi biyu da kotun ta nemi ya biya a matsayin beli.

Sai dai matshin da ake tuhuma ya musanta zargin, daga bisani kuma Dan-Oni ta dage zaman kotun zuwa ranar 23 ga Nuwamba domin ci gaba da sauraron karar.