✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Matsalar tsaro: Kamfanin jiragen saman Azman ya dakatar da jigila a Kaduna

Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan harin da wasu 'yan bindiga suka kai filin jirgin saman.

Kamfanin jiragen saman Azman ya sanar da dakatar da jigila a filin tashi da saukar jirage na Kaduna sakamakon matsalar tsaro da filin jirgin ke fama da ita.

Hakan na kunshe cikin wata sanawa da kamfanin ya wallafa a shafinsa na Twitter, yana bayyana cewa zai dakatar da jigilar matafiya tun daga ranar Litinin din da ta gabata.

Sanarwar ta kara da cewa hukumar kamfanin tuna sane da cewa abubuwa sun daidaita kwanaki kadan bayan harin da ‘yan bindiga suka kai filin jirgin saman jihar inda suka kashe masu gadi da wasu ma’aikata.

Sai dai sanarwar ta ce hukumar kamfanin tana son za ta kara inganta yadda take gudanar da ayyukanta a filin jirgin domin tabbatar da kiyaye rayuka da lafiyar ma’aikatanta da kuma ta fasinjojinta.

Har ila yau kamfanin ya bai wa abokanan huladarsa hakuri tare da bayar da lambar waya domin tuntubarsu idan bukatar haka ta taso.

A ranar Asabar ne dai aka kai wani hari filin jirgin lokacin da  wani jirgin sama na kamfanin AZMAN ke dab da tashi daga filin don tafiya Legas kamar yadda muka wallafa a baya.