✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Matsalolin mata a tsarin rayuwar al’ummar Arewa

Wani bincike da aka gudanar ya gano matsalolin da suka fi ci wa matan Arewacin Najeriya tuwo a kwarya a cikin al’ummarsu. A tattaunawar da…

Wani bincike da aka gudanar ya gano matsalolin da suka fi ci wa matan Arewacin Najeriya tuwo a kwarya a cikin al’ummarsu.

A tattaunawar da wakiliyarmu ta yi da wasu matan yankin a matakai daban-daban a Instagram, sun bayyana irin matsalolin da suke fuskanta a matsayinsu na mata a Arewa.

Matasa da ’yan mata da kuma matan auren sun bayyana wasu abubuwa a cikin al’ummar Hausawa a matsayin babbar barazana ga matan da suka taso har suka girma a cikinta.

— Raina hazakar matan Arewa

A cikin ’yan matan, matsalar da ta fi ci musu tuwo a kwarya ita ce yadda al’umma ke daukar su a matsayin masu rauni kuma marasa kwazo, wadanda ba za su iya cimma baurinsu ba, ko su kai wani mataki ba ko matsayi na aiki ko ilimi.

“Ba ki isa ki yi abun kirki ba sai an ce wani ne ta taya ki….abun haushi,” inji wata matar aure kuma ma’aikaciyar gwamnati mai suna Nassime.

Saboda haka a duk lokacin da wata mace ta samu nasara ko ta cim-ma burinta, sai wasu su rika zargin sai da ta bi wata muguwar hanya kafin ta samu wannan abun.

Idan ta samu wata daukaka ko nasara, ba a ganin cewa kokarinta ne kuma Allah ne Ya kai ta ga wannan matsayi; Sai a dauka cewa dole akwai wani namiji da ya taimaka mata, ko da kuwa babu wani dan Adam da ya ba ta kowace irin gudummawa a kai.

— Gorin rashin aure da wuri

Daga cikin ’yan matan akwai wadanda suka bayyana cewa abin kunya ne yadda muhimmancin da al’ummar Arewa take bayarwa a kan aruensu da zamansu a karksahin namiji.

Sun kara da cewa akwai abin tsaro a irin fifiko da muhimmanci da al’ummar take ba wa maza da abubuwan da suka shafi mazan.

A ganinsu, iyaye sukan dauki auren ’ya mace da mahimmanci sosai ta yadda idan har ’yarsu ta kai wasu shekaru ba tare da ta yi aure ba, sai iyaye su rika nuna damuwarsu, ko ma a rika kwatance da ita ana mata gori a cikin al’umma.

— Tsuke tunani wajen ba su tarbiyya

Suna tsoron idan girmanta ya kai wasu shekaru ba tare da ta yi aure ba — watakila saboda ta tsaya karatun boko ko neman aikin kanta — babu namijin da zai aure ta saboda tunanin za ta fi karfinshi.

Wani wurin da gizo ke saka kuma shi ne hatta tarbiyar ’ya mace a Arewa, ana ba ta ne domin yadda za ta yi zaman aure.

Wasu abubuwan yau da kullum da wadanda suka zama lalura a rayuwar dan Adam, ana koya mata su ne da nufin shirya ta domin ta rika yin su idan ta yi aure, amma ba don ta lakanci yanayin rayuwar yau da kullum ba.

“Idan ba ta yi wani abu ba, sai ki ji ana cewa haka za ki yi a gidan miji idan kika yi aure? Ko ma ki ji ana cewa ya kamata a koya wa wance abu kaza saboda ta fara kaiwa munzalin aure.

“Ba su tunanin nata zabin a rayuwa, sai dai a yi ta tarbiyyantar da ita zuwa lokacin da wani da namiji zai do ya aure ta,” inji wata matashiya da ta bukaci kar a bayyana sunanta.

Wata daliba a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya mai suna Halima, ta ce, “Na ce wa mahaifiyata ina son bulin hanci amma ba ta yarda ba; Ta ce in bari sai na je gidan mijina sai in yi abun da nake so, amma idan ya yarda.

“Ba ka da wani sakewa sai abun da miji yake so, kuma idan kika bi ra’ayinki za su ce kin fara bin abun duniya…”

— Rashin alfahari da su da kin ba su kwarin gwiwa

Wani abun da ke damun matan Arewa shi ne al’ummarsu ba ta cika bayyana kokari da nasarorin da suka samu ko ta yi alfahari da su ba, idan aka kwatanta da yadda al’ummar take nunawa ga al’auran maza.

A wuraren aiki ma ba a ba su mahimamanci yadda ake ba wa maza idan suka samu nasara ko daukaka.

“Shi ke nan mata babu abun da suka iya yi banda girke-girke ne wai?” inji Imaan Muhammad, wata dalibar ajin karshe a matakin digirin farko a Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya.