✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mayakan Ansaru sun kashe ’yan bindiga biyar a Kaduna

Idan ’yan kungiyar Ansaru sun shigo garin sukan ba mu kariya.

Yan bindiga biyar sun yi gamo da karshensu yayin wata arangama da suka yi da ’ya’yan kungiyar Ansaru a garin Damarin dake Karamar Hukumar Birnin Gwari ta Jihar Kaduna.

Wasu mazauna garin Damarin sun shaida wa Muryar Amurka cewa, a daren Litinin din makon nan ne dai ’yan kungiyar Ansarun suka kashe ’yan bindiga biyar.

Mutanen wadanda su ka nemi a sakaya sunan su bisa dalilan tsaro, sun ce suna fama da hare-haren ’yan bindiga a yankin sosai sai dai idan ’yan kungiyar Ansaru sun shigo garin sukan ba su kariya.

Dama dai yankin Damarin na Karamar Hukumar Birnin Gwari na fama da hare-haren ‘yan bindiga na tsawon lokaci, sai dai wasu al’ummar garin sun ce duk lokacin da ’yan kungiyar Ansaru su ka je garin ‘yan bindiganr ba sa samun damar satar mutane da dukiyarsu.

Masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya dai na ganin cewa akwai bukatar daukar matakan gaggawa game da karbuwar ’yan kungiyar Ansaru a wurin al’ummomin yankunan Birnin Gwari don gudun abun da ka iya biyo baya.

Ya ce matukar dai gwamnati ba ta gaggauta daukar matakan magance matsalar tsaro a yankin ba, al’ummomi za su ci gaba da daukaka ’yan kungiyar ta Ansaru tunda suke kare su.

Labarin bayyanar ’yan kungiyar Ansaru a wasu yankunan Jihar Kaduna dai ya dade sai dai Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya ce gwamnati na aiki tukuru kan maganar matsalar tsaro a jihar baki daya.