Daily Trust Aminiya - Mayakan ISWAP sun kashe mutum hudu a Borno
Subscribe

Mayakan ISWAP sun kashe mutum hudu a Borno

Akalla mutum hudu aka kashe ciki har da wani soja daya a wani hari da mayakan Boko Haram suka kai ofisoshin bayar da agaji a garin Damasak da ke Jihar Borno.

Tsagin Boko Haram da ke alaka da kungiyar ISWAP ne suka kai hari ofisoshin da ke kan iyaka da kasar Nijar a ranar Asabar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa AFP ya ruwaito cewa, mayakan ISWAP da suka mamaye Damasak sun cinna wuta a cibiyoyin agaji na kasa-da-kasa.

Sai dai wata majiya kuma ta ce, Cibiyar Majalisar Dinkin Duniya ta kone ne bayan da aka cinna wuta a ofisoshin wata kungiyar agaji ta kasa-da-kasa da ke kusa da ita.

Wannan hari shi ne na biyu cikin watanni biyu da ke shafar daya daga cikin cibiyoyin Majalisar Dinkin Duniya guda tara da ke Najeriya.

A ranar 1 ga watan Maris, mayakan ISWAP suka kai harin wani sansanin Majalisar Dinkin Duniya a Dikwa, inda suka kashe fararen hula shida tare da tilasta wa ma’aikatan agaji tserewa na wani lokaci duk da agajin gaggawa da ake bukata a yankin.

More Stories