✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mazauna karkara sun roki El-Rufai kada ya raba su da mastugunnansu

Gwamnatin Kaduna na shirin sauya wa mazauna yankunan wurin zama.

Mazauna kauyukan Akilibu da Rijana da kuma Katari da ke babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna son roki Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a kan kada ya tashe su daga yankunan nasu.

Al’ummar yankunan sun yi wannan roko ne bayan kudurin da Gwamna El-Rufai ke da shi na sake  musu matsuguni saboda a cewarsa, suna bai wa gaggan barayi mafaka, kuma akwai  da masu kai wa ’yan ta’adda bayanan sirri a cikinsu.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa al’ummomin sun yi rokon ne ta bakin shugaban yankin, Magaji Danjuma-Katari, yayin hira da manema labarai ranar Juma’a a Kaduna.

Danjuma-Katari ya ce, “A iya saninmu, ba mu da masaniyar wani daga cikinmu da ke mu’amala da harkar fashin daji a ciki ko wajen garuruwanmu.

“Don haka zargin da aka yi mana kan cewa muna da taimaka wa ’yan ’yan ta’adda ba gaskiya ba ne.

“Hasali ma, sabanin zargin da ake yi, ba sau daya ba, ba biyu ba, harkokin ’yan bindigar a nan yankunan na karewa ne a kanmu,” inji shi.

Daga nan, ya yi kira da gwamnati da masu ruwa-da-tsaki da a dauki matakan dakile hanyar da ’yan bindigar ke bi a kusa da Katari wajen gudanar harkokinsu.

Kazalika, ya bukaci gwamnati da ta sake duba duka bayanan tsaron da aka gabatar mata masu nasaba da yankunansu don tabbatar da sahihancinsu.