✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mene ne amfanin Jigida da warwaron kafa ga mata?

Sai dai akwai masu yi wa matan da ke amfani da wadannan kayan adon gurguwar fahimta

Jigida kayan ado ne na garjiya da mata ke daurawa a kugu.

Wasu sun ce jigida na taimakawa wajen kiba, kuma tana ba da siffar jiki ga mace.

A daya bangaren kuwa, warwaron kafa, asali kayan adon Indiyawa ne da ake sakawa a cikin kayan aure, inda shi ma mata ne ke amfani da shi.

Sai dai akwai mutanen da ke kallon matan da suke sa warworon kafa a matsayin marasa mutunci, wasu ma har kallon karuwai suke musu, amma mata sun musanta hakan, inda suka ce suna sawa ne saboda ado.

Al’adar Arewa ta ginu ne akan al’adun addinin Musulunci mace, wanda ya ba mace ’yancin yin kwalliya da wadannan kayayyaki, matukar babu wani mutum ban da mijinta da zai gani.

Hatta Alkur’ani mai girma ya haramta wa mata saka kayan ado sai dai ga mazajensu, kuma ba a yarda wani ya ga kwalliyar ba in ba miji ko muharraminta ba.

Aminiya ta tattauna da wasu don sami ra’ayoyinsu kan mata masu amfani da jigida da warworon kafa.

Kabeer Abdul, wani magidanci ya ce Jigida ana amfani da ita da da dadewa a al’adar Hausa domin ado ga mata, amma hatta al’adar ba ta yarda mace ta bude jikinta ba.

“Wannan ya sa ko ta sa sai mijinta ya kamata ya gani. Kananan yara ma ana sa musu jigida. Ado ne na Hausa, ba wani abu ba ne sabanin yadda wasu suke kallon masu amfani da ita kamar karuwai.

“Amma abin da ya sa yanzu ake gani jigida kaman karuwanci ne shi ne mutane galibi yanzu mata su na sawa ne kuma su bar jikinsu a waje.  Hakan ne ya sa Hausawa suke kyamar mace mai sa jigida, saboda za ta bude shi.

“Amma in ba ta bude shi ba sai ga mijinta, babu wata illa. Mafi yawancin maza suna son wannan adon. Ba na ganin jigida kamar wani laifi, in mace za ta yi ado ga mijinta kawai,” inji shi.

A bangaren warwaron kafa kuwa, ya ce mata Indiyawa ne suke amfani da shi.

Sai dai a cewarsa, yanzu lokaci ya zo an canza mishi kallo, inda yanzu mafi yawa ke kallon masu amfani da shi a matsayin alamar wata kungiyar asiri ko kungiya madigo da sauransu.

Ya ce galibi ba a iya bambance tsakanin wadancan mutanen da kuma masu sakawa kawai don ado.

Shi kuwa Najeeb Alhasan cewa ya yi, “Ban dauki cewa sa jigida wani abu ne da zai nuna tana wata kungiya ba, amma kamar ta sa zobe ko warwaro a kafa, wannan ba ya cikin al’adar mutanen Arewa.

“Kamar matan Larabawa suna amfani da shi, amma mace ’yar Arewa ko Bahaushiya ta sa zobe ko warwaro a kafa, gaskiya mutane suna alakanta ta da wasu kungiyoyi ko dabi’u marasa kyau.”

Ita kuwa wata mace, Halima Sani, ta ce “Ni dai na fi son warwaron kafa fiye da jigida saboda yana kara wa mace kyau, kuma ado ne.

“Wasu sunce wai matan da suke sa warwaro a kafa suna cikin wata kungiya, amma ni ban ga wani abu game da hakan ba, kowane dan Adam na da ra’ayinsa,” inji Halima.

Jameela Bashir kuwa ta ce, “Dukkansu kayan ado ne, amma warwaron kafa ya fi kyau, saboda mutane na ganin shi a jikinki, amma jigida wa zai gani in ba mijin ki ba¿. Ni dai ina sa jigida da warwaron kafa.”