✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Miyetti Allah ta bukaci a hukunta masu ta da zaune tsaye ta intanet

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta kasa Reshen Jihar Kaduna ta bukaci Sufeta Janar na ’Yan Sanda ya yi binciken kwakwaf kan wani jawabi…

Kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah ta kasa Reshen Jihar Kaduna ta bukaci Sufeta Janar na Yan Sanda ya yi binciken kwakwaf kan wani jawabi dake yawo a kafafen sada zumunta.

Kungiyar ta ce a wani jawabi da wani mai suna Ardo Bulama ya yi, ya yi zargin cewa Fulani ana shirin kai wa Kiristoci a Kudancin Kaduna muggan hare-hare.

Daraktan Watsa Labaran reshen kungiyar, Ibrahim Bayero Zango ya yi kiran, a martaninsa ga korafin da Dandalin Dattawan Kiristocin Najeriya (NCEF) ta aike wa da shugaban ’yan sandan (kuma aka buga a wata babbar jarida a Najeriya) inda suka bukaci a kamo wanda ya yi barazanar.

Takardar ta ce yunkurin na dattawan abin mamaki ne domin duk wanda ya san sunaye da al’adun Fulani ya san Fulani ba sa amfani da sunan Bulama.

Ta ce abin takaici ne da kungiyar dattawan ta dauki irin jawaban na bogi da ake yadawa da sunan tashin hankali bayan akwai ire-irensu da ake yadawa masu cike da yi wa Fulani barazana da rayukansu.

“Ina son bayyanawa karara cewa shi kan shi jawabin da ake ta yawo da shi a kafafen zamani cewa wani Ardo Bulama ya yi abin zargi ne. Wannan yunkuri ne na bata sunan al’ummar Fulani makiyaya a Najeriya.

“Wannan yana nuna wata mummunar manufar da wasu makiyan Fulani ke son amfani da ita su bata sunan Fulani ba ma ga sauran ’yan Najeriya ba, har ma a idon duniya”.

Sanarwar ta yi kira ga Shugaban ’Yan Sandan da ya gudanar da cikakken bincike tare da kamo wadanda suka kitsa jawabin don a hukunta su.

Yayin da kungiyar ta nesanta kanta daga jawabin da kuma wanda ta ce aka kirkiri sunansa don yin jawabin, ta bukaci al’ummar Fulani a fadin Najeriya da su ci gaba da zama ’yan kasa nagari masu bin doka da oda kamar yadda a ka san su da yi.