✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mu leka yadda NDLEA take arangama da masu dillancin kwaya

Hakan manuniya ce cewa da sauran jan aiki wajen kawar da miyagun kwayoyi a Najeriya.

Hukumar Hana Sha da Dillancin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kasance a sahun gaba wajen hana fataucin kwayoyi a Najeriya.

Hukumar ta samu manyan nasarori sakamakon kusan kowane makon Allah sai an ji amonta a kafafen labarai.

La’akari da yadda hukumar ke samun nasara a kullum, ko a iya cewa Allah san barko ko kuwa akwai sauran rina a kaba?

Aikin da hukumar ta yi kwanakin nan, wanda ya haifar da bankado wani katon dakin ajiyar da ke wani rukunin gidajen da babu jama’a a yankin Ikorodu, Legas, inda ta kwato tan 1.8 (Kilo 1,855) na hodar Iblis da kudinta ya kai Naira biliyan 194.

Hakan manuniya ce cewa da sauran jan aiki wajen kawar da miyagun kwayoyi a Najeriya.

Mai magana da yawun NDLEA, Femi Babafemi, ya ce kwacen da hukumar ta yi ya zama wanda ba ta taka yin irinsa ba a tarihin aikace-aikacenta.

Ya ce hudu daga cikin manyan dillalan kwayoyin har da dan kasar Jamaica daya tare da manajan dakin ajiya.

An kame su ne a wani samamen da aka shirya a tsanake, bayan wasu bayanan sirri.

Aikin ya gudana cikin kwanaki biyu a wurare daban-daban a Jihar Legas.

Madugan dillancin kwayoyin da ke tsare, sun hada da Mista Soji Jibril, mai shekara 69, dan Ibadan Jihar Oyo da Emmanuel Chukwu, mai shekara 65, dan garin Ekwulobia Jihar Anambra da Wasiu Akinade, mai shekara 53, daga Ibadan Jihar Oyo da Sunday Oguntelure, mai shekara 53 daga Okitipupa Jihar Ondo da Kelkin Smith, mai shekara 42, daga Kingston na kasar Jamaica.

Dukkaninsu mambobin wani gungun masu fataucin miyagun kwayoyi ne na duniya, wadda hukumar take bin sawunta tun 2018.

Ma’ajiyar da ke titi mai lamba 6, Lokon Olukuola, rukunin gidajen Solebo, a Ikorodu, jami’an hukumar sun masa dirar mikiya ne a ranar 18 ga Satumbar bana, yayin da aka kamo manyan fataken kwayoyin a otel-otel da makoyarsu daban-daban a sassan birnin Legas.

Binciken farko ya nuna an koye miyagun kwayoyin da suka fi kowane muni a rukunin gidajen, inda daga nan ne gungun nasu yake shirin dillancinsu ga kwastomominsu a sassan duniya daban daban.

An adana kwayoyin ne cikin jakunkuna 10 da kuma durom 13.

Akalla an lalata hodar Ibilis da nauyinta ya kai tan 1.8 da kudinta kuma ya kai Naira biliyan 194 a ranar Talatar makon jiya, bayan samun izinin wata Babbar Kotun Tarayya a Legas.

Da yake magana yayin lalatawa da kone miyagun kwayoyin a yankin Badagry Legas, shugaban hukumar, Birgediya Janar Mohammed Buba Marwa (mai ritaya), ya ce za su ci gaba da shiga kafar wando guda da dillalai da ma kungiyoyin masu fataucin miyagun kwayoyin da ke tafiyar da ayyukansu a Najeriya.

Shugaban, wanda Daraktan kula da harkokin shari’a na hukumar, DCGN Sunday Joseph ya wakilta, ya ce girman hodar Iblis din da aka gano da an kiyasta kudinta kan Dala miliyan 278.25 daidai da Naira biliyan 194, manuniya ce ga girman aika-aikar da masu harkokin miyagun kwayoyin suke tafiyarwa.

Ya ce hakan ya nuna lallai ne ’yan Najeriya su ciga da dafa wa NDLEA a sabon salon yakinta wajen kawar da miyagun kwayoyi a kasar.

A cewarsa, daga cikin tan 1.8 din da aka kwace, an lalata tare da kone kulli 1,828 na hodar Ibilis, yayin da dan abin da ya rage hukumar za ta yi amfani da shi domin shaida, yayin gurfanar da wadanda ake zargin gaban shari’a.

“Yanzu hukumarmu za ta gurfanar da wadanda aka kama da hannu a safarar wannanr hodar Iblis din.

“Ina mai tabbatar wa jama’a cewa NDLEA ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen bin kadun shari’ar har zuwa karshenta.

“Daga 25 ga Janairun 2021, lokacin da muka soma samame kan masu fataucin miyagun kwayoyi, hukumarmu ta yi nasarar da ba ta taka samu ba a tarihi na hukunta wadanda aka kama.

“A halin yanzu, masu safarar kwaya 2, 904 suna garkame a gidajen yari daban-daban na hukuncin laifukansu, sannan akwai wasu kararrakin da kotuna suke sauraron su a halin yanzu da muke da yakinin za mu samu nasara a kansu su ma.

“Bankado mutanen da suke da alhakin koye hodar Ibilis a Ikorodu, sako ne ga gungun masu fataucin kwayoyi cewa jarin da suka zuba a muguwar kasuwa, karshensa konewa zai yi; sannan za su iya rasa ’yancinsu saboda NDLEA ta yanzu fa ta himmatu wajen kame da gurfanarwa tare da tabbatar da an hukunta su.

“Ba a nan muka tsaya ba, za mu kuma bibiyi kadarorin da suka mallaka da haramtattun kudaden,” inji shi.

A cewar Buba Marwa, gudanar da samamen na Ikorodu cikin tsanaki ba tare da fuskantar hayaniya ko zubar da jini ba, wata manuniya ce kan sabon salon hukumar da kuma yadda ta bullo da sababbin dabaru a gudanar da ayyukanta, wanda ya nuna yaki da miyagun kwayoyi ya sake daukar sabon salo.

Ya yaba wa kawayen hukumar na kasashen duniya, musamman takwararta ta kasar Amurka (US-DEA), wacce ta taimaka wajen bankado wannan hodar Ibilis din.

Sannan ya yaba wa rundunar sojojin Najeriya wacce ta bayar da gudunmowar karin jami’an tsaro yayin samamen da sauran hukumomin tsaron da suke dafa wa hukumar a aikinta na kakkabe miyagun kwayoyi a Najeriya.

“Samun lafiyar jama’armu hakki ne da ya rataya a wuyan kowanenmu. Lallai ne kowa ya sauke nauyin da ke kansa ta hanyar dafa wa hukumar wajen tsabtace kauyukanmu da biranenmu ta hanyar shiga sahunmu na Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi mai taken WADA,” inji shi.

Buhari ya taya Marwa murna

Da yake tsokaci kan batun, Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Shugaban NDLEA, Buba Marwa, kan nasarar da ya samu ta wayar tarho daga birnin New York, yayin da yake halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77.

Shugaban ya ce labarin bankado hodar Ibilis din ya faranta masa rai. “Ina matukar jin dadin himmarka wajen kakkabe illar miyagun kwayoyi.

“Abin ya faranta mini rai sosai yayin da nake ci gaba da bibiyar nasarorin da hukumar ke samu karkashin shugabancinka.

“Hakika ka nuna cewa zakar ka domin jagorantar yaki da miyagun dillalan mutuwa, abu ne mai kyau. Don Allah kada ka gajiya,” inji Buhari.

Nasarorin Buba Marwa

Tun bayan da Janar Marwa ya zama shugaban NDLEA, hukumar take samun nasarorin da ba ta taka samu ba a tarihi a fagen yaki da shan miyagun kwayoyi a Najeriya.

Ko gabanin kwato hodar Ibilis din, hukumar a ranar 4 ga Agustan bana ta lalata kilogiram 560,068.31414 na miyagun kwayoyin a yankin Badagry, Legas.

Ta kame mutum 18,940 cikin wata 18 Shugaban na NDLEA ya ce hukumar tana samun nasarar yaki da miyagun kwayoyin tun bayan da ya zama shugabanta daga Janairun 2021 zuwa Yulin bana, inda ta kame mutum fiye da 18,940 da ake zargi da dillancin kwaya.

Cikinsu, maza 17,444 sai kuma mata 1,496, ciki har da giggan masu safarar kwaya su 12.

Sannan ta kuma samu nasara, inda kotu ta yanke hukunci kan mutum 2,904 tare da kwace kwayaoyi da sauran ababuwan maye da nauyinsu ya kai fiye da kilogiram miliyan 3.6.

Ya kuma ce hukumar ta kwace fiye da kadarori 284 da asusun banki 600, tare da toshe asusu fiye da 600 na masu fataucin kwaya, duk dai a tsakanin Janairun 2021 zuwa Agustan bana.

Har wa yau, a ranar 23 na Agustan, jami’an NDLEA sun kame wani mai shara mai suna Ohiagu Sunday, dan shekara 34 a tashar jiragen sama ta Murtala Muhammed da ke Ikeja Legas, wanda ya yi jagora da hada baki da wani gungun masu fataucin kwaya a tashar jiragen.

An kame Sunday bayan kamen wani fasinjan jirgin Air Peace da zai tafi Dubai, Obinna Jacob Osita.

An kame shi da jakunkuna uku, biyu daga ciki suna makare da kunshi takwas na tabar wiwi mai nauyin kilogiram 4.25 da aka koye cikin gari da kifin miya.

An kuma kame wani ma’aikacin tashar jiragen, wanda abokin aikin Sunday ne, sannan jami’an hukumar sun baza komar neman wani mutumin da shi ma ake zargi da hannu a ciki.

A ranar 2 ga Agusta, shugaban ya bayyana a Abuja cewa hukumar ta bankado wasu dakunan gwaje-gwaje guda biyu a jihohin Legas da Anambra, inda ake sarrafa miyagun kwayoyi da wata kwayar da ake kira da sunan Mkpuru Mmiri wadanda ake safarar su a sassan Najeriya har ma da kasashen ketare.

Ya ce samamen ya biyo bayan yadda matasa suke ta’ammali da kuma illar da kwayoyin suke haddasa musu a watanni uku na karshen bara, inda lamarin ya kazance a yankin Kudu maso Gabas.

Ya ce a yayin samamen, an kame kasurguman dillalan miyagun kwayoyi da mai dafa musu abinci.

Sai kuma a ranar 25 ga Satumba, inda nan ma jami’an hukumar suka kame wani tsoho mai shekara 75, mai suna Usman Bokina Bajama (Clemen), tare da wadansu mutum 21 da ake zargi yayin samame daban-daban a jihohi bakwai.

A samamen an kwace kwalaben A Kuskura da da Tiramol da kunshin wani kayan maye guda 1,001,387, tare da tabar wiwi mai nauyin kilogiram 2,536; sannan aka lalata fiye da kadada 10 na gonar tabar a jihohin Edo da Adamawa.

Idan dai za a tuna, wadansu ’yan Najeriya sun nuna damuwa kan yadda ta’ammali da A Kuskura ke samun gindin zama musamman a Arewa, wanda ya zama kayan maye hatta ga wadanda suka manyanta da matan aure.

Yadda duniya take kallon azamar NDLEA

Yayin da cikin shekaru kasashen duniya da ma Ofishin Yaki da Miyagun Kwayoyi da Laifuka na Majalisar Dinkin Duniya (UNODC), suke matukar sa ido kan Najeriya a zaman babbar zangon da masu safarar hodar Ibilis da ta heroyin suke amfani da shi wajen safara zuwa kasuwannin nahiyar Turai da Asiya da Arewacin Amurka, himmar da Gwamnatin Tarayya take yi a baya bayan nan yana samun tagomashi a idon duniya.

Ana alakanta illar miyagun kwayoyi a Najeriya da ruruwar wutar aikace-aikacen masu garkuwa da mutane da karayin daji, musamman ma da a yanzu suke bukatar kwayoyin a matsayin wani kaso na fansar mutanen da suka kama.

Jan aikin da ke gaban NDLEA

Ana ci gaba da shari’ar Abba Kyari, Mataimakin Kwamishinan ’Yan Sanda da aka dakatar, wanda kuma ya jagoranci Rundunar Bankado Miyagu da kai Dauki cikin Gaggawa ta Sufeta Janar na ’Yan Sanda (IRS), tare da wadansu jami’an ’yan sandan guda hudu.

Zargin su da kawance da masu fataucin miaygun kwayoyi, Chibunna Umeibe da Emeka Ezenwanne, wadanda a watan Yuni Kotun Tarayya ta Abuja, karkashin Mai Shari’a Emeka Nwite ta yanke wa hukuncin shekara shida a kurkuku, hakan ya nuna yaki da miyagun kwayoyin ya wuce wanda za a yi a kan tituna kawai.

Kawance da ma gama kai wanda giggan masu safarar kwayoyin suke da shi da abokan huldarsu da ma ’yan barandansu a ciki da wajen Najeriya, manuniya ce cewa sai hukumar ta kara yaukaka kawance da fahimtar juna da abokan huldarta na kasashen duniya kan yaki da miyagun kwayoyin.

Sakayya ga namijin kokari

Domin kara inganta aikaceaikacenta, NDLEA ta yi wa wadansu manya da kananan jami’anta karin girma.

Wani kwararre kan tsaro kuma mai fafutika kan miyagun kwayoyi, Shola Mese, wanda ya yi kiran da a kara daukar kwararrun ma’aikata a hukumar ta NDLEA, ya ce ma’aikatan da hukumar take da su a yanzu sun yi kadan.

“Kalubalen bai tsaya a nan kawai ba, a galibin jihohi babu ingantattun motoci da makaman da jami’an hukumar za su yi aiki da su wajen tunkarar masu safarar miyagun kwayoyin nan ko kuma su kai su zuwa kotuna,” inji Mese.

Naira miliyan 580 domin sayo motocin sulke

A yunkurin karfafa yaki da miyagun kwayoyin, Majalisar Zartarwa ta Kasa (FEC) ta sahale Naira miliyan 580.5 domin sayen motocin sulke guda hudu ga hukumar ta NDLEA.

Ministan Shari’a, Abubakar Malami, shi ya bayyana hakan a ranar Larabar makon jiya, bayan taron majalisar da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Abuja.

“Adadin kudaden kwangilar shi ne Naira miliyan 580.50, ciki har da Harajin Kayayyakin, inda za a kawo motocin nan da makonni 16,” inji Malami.

Ya kara da cewa an ba da kwangilar ce da zimmar karewa tare da karfafa gwiwar jami’an hukumar ta NDLEA.