✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mu Sha Dariya: Bazazzagi a Kano

Yaro ko da me ka zo an fi ka..

Wani Bazazzagi ne ya ce shi fa bai yarda cewa Kano ta Dabo tumbin giwa ba ce, ballantana ma a ce yaro ko da me ka je an fi ka.

Dalilin wannan kira da ake yi wa Kano ya ce zai je da tasa hikimar domin ya ga ko zai samu gaba da shi.

Ya samu wani akwatin katako cike da tangaran ya dauka ya tafi Kano a mota.

Da aka sauke shi a tasha ya ce waye zai daukar masa akwatin ya kai masa gida amma fa ladansa shi ne wasu maganganu guda uku na gaskiya wanda in ya rike su za su yi masa amfani.

Da yake ba a fahimce shi ba sai ake yi masa dariya amma can sai wani dan dako ya zo ya ce zai dauka amma in ya ji ba su gamsar da shi ba, shi kuma zai fada masa magana guda wadda ta fi ukun nasa.

Ya amince, dan dako ya dauki akwati suka fara tafiya.

Da suka dan yi tafiya sai dan dakon ya ce: “Fada mini guda in ji.”

Bazazzagi ya ce: “Kowa ya ce maka da koshi gara yunwa, kada ka gaskata shi.”

Da suka yi rabin tafiyar sai dan dakon ya ce: “Fada min ta biyu na ji.”

Bazazzagi ya ce: “Kowa ya ce ma da tafiya a kan abin hawa gara kafa kada ka gaskata shi.”

Da suka je kofar gidan sai Bazazzagi ya ce: “Cikon maganarka ta uku ita ce, kowa ya ce ma za a ba ka ladan dakon nan kada ka gaskata shi.”

Sai dan dakon ya ce: “Yaro ko da me ka zo an fi ka.”

Sai ya saki akwatin tangaran din nan ya fadi kwatsam! Sannan ya ce wa Bazazzagi: “Kowa ya ce ma akwai tangaran mai rai a cikin akwatin nan kada ka gaskata shi.”