✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Muhimman abubuwan da su ka faru a makon jiya

A makon da ya gabata dai an sha tirka-tirka iri-iri, kama daga rikicin jam’iyyar APC mai mulki, rikita-rikitar siyasar jihar Edo, rasuwar tsohon gwamnan Oyo…

A makon da ya gabata dai an sha tirka-tirka iri-iri, kama daga rikicin jam’iyyar APC mai mulki, rikita-rikitar siyasar jihar Edo, rasuwar tsohon gwamnan Oyo Abiola Ajimobi sanarwar Saudiyya cewa a bana ‘yan cikin kasar ne kawai za su yi aikin Hajji da dai sauransu.

Aminiya ta tattaro muku kadan daga cikin muhimman labarum na makon jiya:

 

‘Yan cikin Saudiyya ne kadai za su yi aikin Hajji a bana

An takaita aikin Hajjin bana zuwa mazauna Saudiyya kadai
Mahajjata suna Sa’ayi tsakanin Safa da Marwa a Saudiyya

A farkon makon da ya gabata ne Ma’aikatar Aikin Hajji da Umara ta Saudiyya ta sanar cewa a bana mutanen da ke cikin kasar ne kadai za su gudanar da ibadar aikin Hajji.

Matakin na zuwa ne bayan an jima ana muhawara a kan yiwuwar gudanar da ibadar a bana, sakamakon annobar coronavirus.

Hakan dai na nufin bana alhazai ‘yan asalin kowace kasa za su yi aikin Hajjin matukar suna cikin Saudiyya kafin fitowar sanarwar.

‘Yan asalin Saudiyya da ke wasu kasashe ba za su samu damar yin ibadar ba, wadda aka takaita yawan alhazan na bana zuwa kimanin dubu goma.

A bara alhazai sama da miliyan biyu ne suka shiga kasar daga kasashen duniya daban-daban don aikin na Hajji.

 

Rikicin APC ya kara kazancewa

Biyo bayan umarnin wata kotu da ya dakatar da Adams Oshiomhole daga shugabancin APC, Mataimakin Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Victor Giadom ya nada kansa ya kuma maye gurbin Oshiomhole, bayan Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa (NWC) ya nada Hilliard Eta.

An samu turjiya tsakanin bangarorin, kowanne na sanar da dakatar da dayan, har ta kai ga ‘yan sanda sun rufe hedikwatar jam’iyyar, bayan shugaba Buhari ya nuna goyon bayansa karara ga shugabancin na Giadom.

Mutane da dama dai na ganin cewa ayyana goyon bayan na Giadon da Buhari ya yi tamkar yankar baya ne ga tsagin tsohon gwamnan jihar Legas kuma jagoran jam’iyyar, Bola Tinubu.

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa, Adams Oshiomhole

Daga baya dai shugaba Buharin ya sanar da rushe shugabancin jam’iyyar tare da nada gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a matsayin shugaban kwamitin rikon kwarya da zai gudanar da babban taro da zaben sabbin shugabannin jam’iyyar.

Daga bisani kuma Oshiomhole ya mika wuya ya yi mubaya’a ga shugabancin na riko.

 

Rikita-rikitar siyasar jihar Edo

Biyo bayan matakin da jam’iyyar APC ta dauka na haramta wa Gwamna Godwin Obaseki damar sake tsayawa takarar kujerarsa gwamnan ya sanar da ficewa daga jam’iyyar.

Daga bisani kuma da wata kotu ta dakatar da shi daga shiga zaben fida da gwani na jam’iyyar PDP. Ko da yake daga bisani wata kotun ta jingine wancan hukuncin, inda a karshe dai ya sami nasarar lashe zaben tare da kasancewa dan takarar jam’iyyar ta PDP.

Godwin Obaseki ya koma PDP
Gwamnan Edo Godwin Obaseki lokacin da ya koma jam’iyyar PDP

Kazalika, Pastor Osagie Ize-Iyamu ya sami nasarar lashe zaben na fid da gwani ajam’iyyar APC.

 

Rusa ofishin jakadancin Najeriya da ke Ghana

A dai cikin makon jiyan ne Ghana ta ba wa Najeriya hakuri tare da alkawarin sake ginawa da mallaka wa Najeriya ginin Ofishin Jakadancinta da ke Birnin Accra na kasar Ghanan bayan wasu matasa dauke da makamai sun far wa ofishin suka rusa wani bangarensa.

Ghana ta nemi afuwar Najeriya bayan 'yan bindiga sun rusa ofishin jakadancin Najeriya a birnin Accra
Sashen ofishin jakadancin Najeriya da ‘yan bindiga suka rusa a Ghana

Rahotanni sun ce matasan sun yi hakan ne biyo bayan takaddama kan mallakin wani bangaren filin da aka yi ginin, inda wani attajiri dan kasar ya yi ikirarin cewa ginin ya shiga cikin filinsa.

 

Rasuwar tsohon gwamnan Oyo, Abiola Ajimobi

A ranar Alhamis da ta gabata iyalan tsohon gwamnan jihar Oyo, Sanata Abiola Ajimobi suka sanar da rsuwarsa bayan fama da rashin lafiya.

Dan kimanin shekaru 70, marigayi Ajimobi dai ya jagoranci jihar Oyo na tsawon shekaru takwas daga shekara 2011 zuwa 2019.

Tsohon gwamnan jihar Oyo, Marigayi Abiola Ajimobi

An yi jana’izarsa ranar Lahadi a gidansa da ke Ibadan babban birnin jihar.

 

Ceto leburori 126 da aka kulle a kamfanin shinkafa a Kano

A yammacin ranar Litinin da ta gabata ne ‘yan sanda a Kano suka yi dirar mikiya a wani kamfanin sarrafa shinkafa mai suna Popular Rice Mill da ke Kano tare da ceto akalla leburori 126.

Makwancin da leburorin a sadda suke kulle a masana’antar

Ana zargin kamfanin ya kulle ma’aikatan ne tsawon watanni uku ba tare da barinsu su fito ko kofarsa ba.

Leburorin sun yi zargin azabtarwa tare da cin zarafi daga hukumomin kamfanin, ko da yake sun musanta hakan.

 

Sake bude filin jirgin saman Abuja

A ranar Asabar din makon jiya ne hukumomi suka sanar da sake bude filin jirgin sama na Nnamdi Azikwe da ke birnin tarayya Abuja bayan shafe tsawon lokaci a rufe sakamakon annobar coronavirus.

Sabon tsarin yadda za a rika bin layi a filin jirgin sama

 

NYSC ta ce babu ranar sake bude sansanoni

Hukumar Kula da Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima (NYSC) ta ce babu takamaiman ranar sake bude sansanonin bayar da horo.

NYSC: Babu ranar bude sansanoninmu
Matasa Masu Yi Wa Kasa Hidima

A watannin baya ne dai hukumar ta rufe sansanonin saboda barazanar annobar coronavirus.

 

Liverpool ta lashe gasar Premier

Bayan kimanin shekaru 30, kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta sami nasarar lashe gasar Premier.

‘Yan wasan kungiyar Liverpool suna murna

Hukumar gasar ta bayyana hakan ne bayan kungiyar Chelsea ta lallasa mai biye wa Liverpool din a matsayi na biyu, Manchester City da ci 2-1 a ranar Alhamis.

 

An bude rijistar shirin N-Power           

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Ma’aikatar Jinkai da Agajin Gaggawa ta sanar da bude shafinta don dibar sabbin matasa a karkashin shirinta na samar da aikin yi ga matasa na N-Power. Kasa da awa 48 da bude shafin a intanet, matasa fiye da miliyan daya ne suka yi rijista.

Ma’aikatar dai ta ce za ta sallami rukunin farko da na biyu na matasan dake cikin shirin domin samun dibar sababbi.

 

An yaye kuratan sojoji kusan 5,000

Sabbin sojoji 4,918 da suka sami horo daga makarantar horas da kuratan soji ta Najeriya (Depot) da ke Zariya ne aka yaye ranar Asabar a wani buki mai kayatarwa da aka gudanar a filin fareti na Kim Hamma da ke barikin.