✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun ceto mutum 100 daga kangin bauta  —Masari

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta ceto fiye da mutum 100 daga kangin bauta cikinsu har da kananan yara da aka kai almajiranci a wurare…

Gwamnatin Jihar Katsina ta ce ta ceto fiye da mutum 100 daga kangin bauta cikinsu har da kananan yara da aka kai almajiranci a wurare daban-daban ciki har da Abuja.

Daga cikin mutane da aka ceto daga kangin bautar har da wasu mutum 26 da aka kai kasar Burkina Faso da sunan za a samar musu da ayyukan yi amma suka kare da fadawa cikin wannan hali.

Jihar ta ce ta bi dukkannin hanyoyi, har ta tura wakilai da wasu jami’an shigi da fici Burkina Faso don dawo da mutanen ta kuma sada su da iyalansu.

Mai ba Gwamna Aminu Masari Shawara kan Yaki da Miyagun Kwayoyi da Safarar Bil Adama, Hamza Burodo ne ya fadi haka a taron fadakarwa kan dakile ta’ammuli da miyagun kwayoyin da safarar mutane da ofishinsa ya shirya wa kungiyoyin sufuri da suka hada da NURTW, NARTO, masu haya da Keke NAPEP, ’yan acaba, jami’an tsaro da sauran masu ruwa.

Shugaban kungiyar NURTW na Jihar Katsina, Musa ’Yandoma, ya jinjina wa Gwamna Masari a kan wannan tunani na wayar da kan jama’a a kan wannan muguwar dabi’a.

Shi ma Alhaji Muhammadu Usman Sarki daya daga cikin masu ruwa da tsakin, ya yi addu’ar Allah Ya kawo karshen wannan masifa.

Taron na yini daya, an gudanar da shi a ne babban dakin taro na Ma’aikatar Kananan Hukumomi a garin Katsina kuma ya samu halarcin wakillan Masarautar Katsina da Daura da kungiyoyin da aka gayyata.