✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun fi samun kayan aiki a lokacin Buhari – Babban Hafsan Sojin Kasa

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Farouk Yahaya, ya ce yanzu sojojin sun fi samun karfin gwiwa tare da kayan aiki a karkashin…

Babban Hafsan Sojin Kasa na Najeriya, Laftanar Janar Farouk Yahaya, ya ce yanzu sojojin sun fi samun karfin gwiwa tare da kayan aiki a karkashin mulkin Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari fiye da kowane lokaci.

Ya kuma ce kwazon aiki da kwarewa na Rundunar Sojojin Najeriya ya samu ci gaba sosai a karkashin gwamnatin Buharin.

Yahaya ya bayyana hakan ne a jawabinsa na rufe gasar kananan makamai na sojojin Najeriya na shekarar 2022 da aka gudanar a shiyya ta uku ta rundunar da ke barikin Maxwell Khobe a Rukuba Jos.

Ya ce, ana gudanar da gasar ne a duk shekara, wanda ke nuna samar da dabarun yaki a tsakanin sojojin kasar.

“A cikin shekarun da suka wuce, gasar ta taimaka wajen samar da wasu daga cikin mafi hazaka a cikin nau’o’i daban-daban da kuma karfafa wasu don kara kwazo da inganta kwarewar harbi,” in ji shi.