✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun karbo bashin $800m don rage radadin tallafin man da za mu cire – Gwamnati

Ta ce za a cire tallafin ne a watan Yuni mai zuwa

Gwamnatin Tarayya ta ce ta karbo bashin Dalar Amurka miliyan 800 daga Bankin Duniya domin raba wa ’yan kasa su rage radadin tallafin man da take shirin cirewa.

Ministar Kudi, Kasafi da Tsare-tsare, Zainab Ahmed, a yayin taron Majalisar Zartarwa ta Kasa ranar Laraba ta shaida wa wakilinmu cewa yanzu haka kudaden suna hannu, kuma dab ake a fara raba su.

Ta ce, “Game da batun cire tallafin man fetur, wannan lamari ne da ya shafi sabuwar Dokar Man Fetur ta Kasa. Dokar ta tanadi cewa dole a cire duk wani tallafi a bangaren man, wata 18 bayan aiwatar da dokar. Wata 18 kuma zai kare ne a watan Yunin 2023.

“Bugu da kari, muna nan muna shirye-shiryen ganin tsarin kashe kudadenmu na matsakaicin zango ya yi aiki kan batun cire tallafin yadda ya kamata. Tuni shirye-shriye suka gama kankama.

“Mun samo wani bashi daga Bankin Duniya, kuma abin da za mu yi ya hada da bayar da wani tallafin kudi ga ’yan Najeriya masu karamin karfi har iyalai miliyan 10. Iyalai miliyan 10 kuma na nufin akalla mutum miliyan 50 ke nan.

“Amma muna kokarin fito da kwararan hanyoyi don ganin ba wai kawai tura kudade ga jama’a muka yi ba, muna da wasu tsare-tsaren tallafin bayan wannan.

“Alal misali, kungiyoyin kwadago za su bukaci motocin sufuri ga mambobinsu. Akwai abubuwa da dama da muke shiri a kansu. Wasu nan take za mu fara su, wasu kuma na bukatar lokaci,” in ji Ministar.

Da aka tambaye ta ko gwamnati mai jiran gado ta san da maganar cire tallafin, sai ta ce akwai tattaunawa iri-iri da suke yi da kwamitin karbar mulki, kuma a matakai daban-daban.