✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun kwato shanu 300 daga hannun barayi a dare daya – Gwamnan Zamfara

Gwamna ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ya ce kauyen da ma wani sashe na Gusau na kokarin zama maboyar bata-gari.

Gwamnatin jihar Zamfara tare da hadin gwiwar jami’an tsaro a jihar sun sami nasarar kwato shanu 300 daga barayi a daren ranar Asabar kawai.

Gwamnan jihar, Bello Matawalle ne ya sanar da hakan ranar Lahadi, lokacin da ya karbi bakuncin masu kafafen watsa labarai a wani taron bude-baki a gidansa dake Gusau, babban birnin jihar.

 A cewar Gwamnan, “Mun sami wasu bayanan sirri a kan hanyoyin da barayin shanun suka bi a daidai kauyen Kuraji dake kusa da Gusau, inda ba mu yi wata-wata ba muka aike da jami’an tsaro suka cim musu.

“Ko da suka hangi tarin jami’an tsaron sai suka cika wandunansu da iska, suka fantsama dazuka suka bar shanun a nan, wadanda aka kawo su Gusau.

“Nan ba da jimawa ba za mu yi sanarwa domin masu su su zo su karbe su,” inji shi.

Gwamna Matawalle ya kuma nuna takaicinsa matuka kan yadda ya ce kauyen na Kuraji da ma wani sashe na Gusau na kokarin zama maboyar bata-garin, musamman masu garkuwa da mutane, inda ya ce duk wanda ya shigo hannu daga cikinsu zai dandana kudarsa.

Daga nan sai Gwamnan ya yi kira ga jama’a da a ko da yaushe su taimaka ta hanyara samar da bayanan sirri ga jami’an tsaro wanda ya ce hakan zai taimaka matuka wajen kakkabe su.

Tun da farko a nasa jawabin, shugaban Kungiyar ’Yan Jarida na Najeriya (NUJ) reshen jihar, Bello Boko, ya godewa Gwamnan saboda shirya musu bude-bakin wanda ya ce shine irinsa na farko tun da ya zama Gwamnan jihar.