✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mun yanke duk wata alaka ta tsaro da Nijar — Tarayyar Turai

Mun dakatar da duk wani tallafi na kudi da muke bai wa Nijar.

Kungiyar Tarayyar Turai ta ce ta yanke duk wata hulda a kan abin da ya shafi tsaro tare da dakatar da duk wani tallafi na kudi da take bai wa Nijar, biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a kasar.

Jagoran manufofin hulda da kasashe na Tarayyar Turai, Josep Borrell ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.

Wadanda suka yi wannan juyin Mulki na Nijar dai sun ayyana Janar Abdourahamane Tiani a matsayin shugaban kasa a ranar Juma’a, bayan da suka wancakalar da shugaba Mohamed Bazoum.

Tarayyar Turai, Amurka da sauran kasashen duniya sun yi kira da a saki shugaba Bazoum ba tare da gindaya wasu sharruda ba, kana a maido da Mulki dimokuradiyya a kasar.

Nijar ce kasar da ta fi samun tallafi daga kasashen yammacin Turai, kuma babbar abokiyar aikin Tarayyar Turai a wajen yaki da bakin haure da ke bi ta Sahara zuwa nahiyar Turai.

Bugu da kari, Tarayyar Turai tana da dakaru da ke aikin bada horo a Jamhuriyar Nijar.

Kungiyar Tarayyar Turai ta wallafa a shafinta na intanet cewa ta kasafta kudin da ya kai Yuro miliyan 503 tun daga shekarar 2021 don bunkasa sha’anin mulki da ilimi a Jamhuriyar Nijar.