✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna cikin fargaba da damuwa —Ma’aikatan lafiya a Kano

Tun bayan da aka ce likitoci 10 sun kamu da coronavirus a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), ma’aikatan lafiya a asibitin da ma jihar…

Tun bayan da aka ce likitoci 10 sun kamu da coronavirus a Asibitin Koyarwa na Aminu Kano (AKTH), ma’aikatan lafiya a asibitin da ma jihar Kano gaba daya suka afka cikin fargaba da tsoron yiyuwar kamuwa da cutar.

Shugaban Kungiyar Likitoci a asibitin, Dokta Abubakar Nagoma, ya shaida wa manema labarai cewa likitocin sun kamu ne yayin da suke duba marasa lafiya.

Haka kuma ya ce a yanzu haka takwas daga cikin likitocin suna cibiyar killace wadanda suka kamu yayin da biyu daga ciki suka killace kansu a gidajensu saboda alamomin cutar ba su bayyana a jikinsu ba.

Dokta Ibrahim Musa likita ne a bangaren jini na asibitin.

Damuwa da yadda abin ke ta’azzara

Ya ce kasancewar suna sane da cewa akwai yiyuwar su kamu da cutar a matsayinsu na ma’aikatan lafiya, amma a wannan lokaci sun fi shiga damuwa duba da yadda cutar ke kara ta’azzarar a tsakanin alumma.

“Kowa ya san akwai hatsari a yanayin aiki musamman ita wannan cuta ba a saurin gane ta, ba kamar wasu cututtuka irin su kwalara da sauransu ba.

“Kuma kashi 60 cikin 100 na marasa lafiya da ke zuwa asibiti suna zuwa ne a kan ire-iren alamomin wannan cutar da suka hada da zazzabi. To kin ga ba za ka iya ware wasu ka ce suna dauke da cutar ba.”

Akasi ake samu

Dokta Ibrahim ya kara da cewa, “su kansu likitocin da suka kamun akasi ake samu a lokacin da suke duba marasa lafiya.

“Wasu marasa lafiyar ba su da takunkumi saboda tsadarsa wasu kuma suna boye bayanan da ya kamata su bayyana don tsoron kada a rika guje musu”.

A cewarsa shi a kan kansa yakan dauki matakan kariya ta hanyar sanya takunkumi da kuma bayar da tazara tsakaninsa da marasa lafiya.

“Nakan auna zafin jikin mara lafiya daga nesa. Idan kuma ya zama dole sai na taba mara lafiya to ina amfani da safar hannu.

“Kamata ya yi a rika amfani da rigar kariya, amma saboda tsadarta hakan ba ya yiyuwa domin ba ta da yawa a asibiti. Kuma ba zai yiyu maras lafiya ya iya biyan kudinta a cikin kudin da zai biya ba”, inji shi.

‘Ba mu da zabi’

Bashir Ado Ali ma’aikacin jinya ne a Asibitin Aminu Kano ya bayyana cewa duk da cewa akwai hatsarin kamuwa da cutar a yanayin aikinsu amma hakan ba ya hana su gudanar da aikin..

“Hatsari babba kuwa domin ba ka san mara lafiyar da kake mu’amala da shi ba.

“Kadan daga ciki ne ake iya gane yanayinsu kuma ake killace su.

“To amma duk da haka dole ne mutum ya yi iyakar kokarinsa wajen bayar da guddumawa domin idan ba mu yi ba. Babu wanda zai yi.

“Abin da ke akwai kawai shi ne muna kokarin daukar duikkanin matakan kariya da suka kamata ta hanyar yin amfani da man goge hannu da sanya safa da takalman roba da sauransu”.

Shi ma Dokta Murtala Umar likita ne a dakin harhada magumguna na Asibitin Aminu Kano wanda ya bayyana cewa ma’aikata suna cikin hatsari saboda yadda ake samun karuwar cutar a tsakaninsu su kuma suke sanya wa iyalansu.

Hadari ga iyali

“Babban abin damuwar shi ne yadda idan mutum ya dauki cutar ba iya kansa abin zai tsaya na, har  iyalansa. A yazu haka akwai abokin aikinmu da yake cibiyar killace wadanda suka kamu tare da ’ya’yansa uku. An yi sa’a matarsa da wani dan nashi ba su kamu ba.”

Ya kara da cewa babbar matsalar da ake fuskanta ita ce rashin kayan kariya ga maikatan lafiya.

“Kin san duk abin da mutum zai yi sai yana da lafiya. Idan da za a ce gwamnati za ta samar da kayan kariya ga ma’aikatan lafiya, wallahi a shirye suke su yi aikinsu domin ba su da wani aikin sai wannan.”

Ma’aikatan lafiya da dama ne dai tsautsayi ya hau kansu suka kamu da coronavirus a Nigeria