✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Muna rokon Saudiya ta ceto duniya daga karancin man fetur —Boris Johnson

Turai na son maye gurbin man fetur din Saudiyya da wanda Rasha ke sayar musu a baya.

Firaministan Birtaniya Boris Johnson, ya roki kasar Saudiya mai arzikin man fetur ta kara yawan man da ta ke kai wa Turai don maye gurbin wanda Rasha ke sayar musu a baya, biyo bayan takunkuman da suka kakaba wa Moscow da ya hana cinikayya tsakaninsu saboda yakinta a Ukraine.

Johnson ya mika kokon barar ne yayin da ya gana da Yarima mai jiran gado na Saudiya Mohamed bin Salman a wata ziyarar kokarin wadata Turai da man fetur da jagoran na Landan ya ke yi a kasar.

Ziyarar ta Boris Johnson da ya faro tun daga ranar Laraba, ita ce irinta ta farko tun bayan tsanantar rikicin Riyadh da Turawan Yamma biyo bayan kisan dan jarida Jamal Kashoggi.

Bayan kammala ganawar jagororin biyu, Boris Johnson ya shaidawa jaridun Birtaniya cewa ya yi tattaunawa mai armashi tsakaninsa da MBS kan yadda Saudiya za ta yi kokari wajen hana katsewar makamashi a Turai da kuma taimawa wajen warware rikicin Ukraine.

A cewar Johnson sun kulla yarjeniyoyi masu muhimmanci a ziyarar, wadanda za su taimakawa ba kadai Birataniya ba har ma da sauran kasashen duniya da kuma ceto kasuwar man fetur daga rikicewar farashi.

Birtaniya na son Saudiya ta kara yawan man da ta ke fitarwa kasuwannin Duniya don dakile barazanar karancinsa saboda rashin mai daga Rasha wanda tuni ya fara haddasa gagarumar matsala musamman ga kasashen Turai.

Boris Johnson ya koka da yadda farashin man ya tashi daga dala 100 kan duk ganga guda kafin fara yakin Rasha a Ukraine zuwa dala 120 a yanzu.

Bayanai sun ce ziyarar ta Boris Johnson ita ce irinta ta farko da wani shugaba daga Turai ya kai kasar jagorar larabawa tun bayan kisan Jamal Kashoggi a shekarar 2018, kisan da aka dora alhakinsa kan Mohamed bin Salman ko kuma MBS.