✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutane Miliyan 1 ne ke fama da matsananciyar yunwa a Sri Lanka

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 1.5 ne a Sri Linka suke fama da matsananciyar yunwa, sakamakon karancin abinci da kasar ke fama…

Majalisar Dinkin Duniya ta ce akalla mutane miliyan 1.5 ne a Sri Linka suke fama da matsananciyar yunwa, sakamakon karancin abinci da kasar ke fama da shi.

Cikin wata sanarwa da majalisar ta fitar karkashin shirinta na tallafawa kasashenn duniya da abinci, ta ce matsin tattalin arziki da Sri Lanka ke ciki ya jefa kashi 3 bisa goma na al`ummar kasar cikin matsananciyar yunwa.

Baya ga wancan adadi, akalla wasu mutane miliyan 6.3  na bukatar tallafin abincin.

Kazalika ta ce za ta yi amfani da tsare-tsaren bada tallafi da kasar ke da su yanzu haka, domin isa ga kananan yara, da su ma suka fada cikin wancan rukunin.

Kasar dai na fama da matsin tattalin arziki mafi muni a baya-bayan nan, sakamakon karancin kudaden waje, da ya janyo rashin shigo da kayan masarufi da fetir har ma da magunguna cikinta.