Daily Trust Aminiya - Mutanen gari sun kona ’yan bindiga a Kano

Tsohuwar ajiya.

Mutanen gari sun kona ’yan bindiga a Kano

Mutanen gari sun babbaka wasu ’yan bindiga har lahira a kauyen Rimi da ke Karamar Hukumar Sumaila ta Jihar Kano.

An cinna wa mutanen, wadanda ake zargin ’yan fashi ne, wuta bayan ’yan bindigar sun kutsa cikin garin, amma matasa suka fatattake su.

Rahotanni daga garin Rimi sun ce ’yan fashin su uku sun addabi yankin, amma matasan gari sun yi nasarar rutsa su, suka cafke biyu daga cikinsu, amma na ukun ya tsere.

Sai da fusatattun matasan suka lakada wa ’yan fashin duka sannan suka rataya wa kowannensu taya, suka cinna masa wuta, har sai da suka kone suka zama toka.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce Rundunar ta samu rahoto cewa wasu fusatattun mutane sun cinna wa wasu ’yan fashi biyu wuta, amma na ukun ya tsere.

‘Sun zama toka’

DSP Kiyawa ya ce ko da ’yan sanda suka isa wurin, ’yan fashin sun riga sun zama toka, sai dai kawai suka kwashe su zuwa asibiti.

“Mun gano wukake da sauran makamai da ake zargin na ’yan fashin ne.

“Kwamishinan ’Yan Sanda na Jihar Kano, Samaila Shuaibu Dikko, ya ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike a kan lamarin,” inji shi.

DSP Kiyawa ya bukaci jama’a da su daina daukar doka a hannunsu saboda kar wata rana su kashe wanda ba bai ji ba, bai gani ba.

Ya bukace su cewa duk lokacin da suka kama wanda ake zargi su mika shi ga ’yan sanda su gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Karin Labarai