✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutum 2 sun mutu, 11 sun jikkata a hatsarin mota a Bauchi

An ajiye gawar wadanda suka mutu kafin kammala bincike.

Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) a Jihar Bauchi ta tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkatar wasu 11 a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a yankin Sabon Garin Nabardo da ke kan hanyar Jos zuwa Bauchi.

Kwamandan hukumar a jihar, Yusuf Abdullah, ya shaida wa Aminiya cewa, hatsarin ya auku ne a ranar Litinin da misalin karfe 7:50 na dare a Sabon Garin Nabardo, wanda ya hada da wata mota kirar Vectra Opel da kuma wata Pegueot 406, wanda ya rutsa da mutum 13 a cikin motoci biyu.

Abdullahi ya bayyana cewa an kai gawarwakin da wadanda suka mutu zuwa babban asibitin Toro, inda likita ya tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da jikkatar mutum 11.

A cewarsa, wadanda suka ji rauni suna asibitin ana ba su kulawa.

Abdullahi ya kara da cewa, an killace gawarwakin a dakin ajiyar gawa na babban asibitin Toro kuma za a mika su ga iyalansu da zarar an kammala bincike.