✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 20 sun mutu a hatsarin mota a hanyar Kaduna zuwa Abuja

Ana zargin gyangyadin da direban ke yi ne musabbabin hatsarin

Akalla mutum 20 ne aka tabbatar da rasuwar su sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru tsakanin tirela da motar bas a kan babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja.

Bayanai na nuni da cewa daga cikin wadanda hatsarin ya ritsa da su, 17 maza ne, biyu mata sai kuma karamin yaro, yayin da mutum biyu suka tsallake rijiya da baya.

Hatsarin dai ya faru ne wajen misalin karfe 5:00 na safe, lokacin da bas din ta daki tirelar wacce ke ajiye a gefen hanya.

Shugaban Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC) reshen Jihar Kaduna, Hafiz Muhammad ya tabbatar da faruwar hatsarin.

Ya ce suna zargin cewa gyangyadin da direban motar ke yi ne saboda tafiyar dare ne musabbabin hatsarin.

Hafiz ya ce, “Bas din ta fada karkashin tirelar siminti ta kamfanin BUA, sannan ta kama da wuta. Akwai mutum 22 a cikinta, inda 20 daga ciki suka mutu.

“An ce tirelar a ajiye take lokacin da bas din ta je ta dake ta, ta kuma shige karkashinta. Abin tsoro ne matuka kasancewar a kullum muna gargadin direbobi kan tafiyar dare,” inji shi.

Shugaban hukumar ta FRSC ya ce ko da yake babu wata doka da ta hana tukin dare kai tsaye, amma tana da matukar matsala saboda kusan dukkan haduran da ake yi a hanyar tafiyar daren ce ke haddasa su.