✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 6 sun mutu a harin ’yan bindiga a Kaduna

Mutum shida sun mutu, wasu da dama kuma sun samu rauni sakamakon harin ’yan bindiga a Kananan Hukumomin Chikun da Giwa Jihar Kaduna ranar Asabar.…

Mutum shida sun mutu, wasu da dama kuma sun samu rauni sakamakon harin ’yan bindiga a Kananan Hukumomin Chikun da Giwa Jihar Kaduna ranar Asabar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce maharan sun kashe mutum biyu a yankin Maskoro da ke Kakau da wasu biyu a Akunakwo da ke Gwagwada, duk a Chikun.

Sai kuma wasu mutum biyu da aka kashe a tsakanin Hayin Inji da Kidandan da ke Karamar Hukumar Giwa.

Kwamishinan ya kuma tabbatar da mutuwar mutu daya da jikkatar wasu mutum tara a harin ranar Juma’a a yankin ’Yan Rake da ke Galadimawa a Karamar Hukumar Giwa inda ’yan bindiga suka rika harbi kan mai uwa da wabi suka kuma jefa abin fashewa.

“Gwamna Nasir el-Rufai ya kadu da samun wadannan labaran yana kuma addu’ar samun rahama ga mamatan tare da jajanta wa iyalansu.

“Ya kuma bukaci jami’an tsaro da su sake zage damtse domin dakile sake aukuwar hakan a jihar,” inji shi.