✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mutum 600 sun mutu a hatsarin mota a titin Kano zuwa Kaduna cikin wata 6 — FRSC

FRSC ta kuma ce karin wasu 2,319 sun jikkata sanadiyyar haduran

Alkaluma sun nuna akalla mutum 600 ne suka rasu, wasu 2,310 kuma suka sami raunuka a hatsarin mota a kan titin Kano zuwa Zariya zuwa Kaduna cikin watanni shida na farkon wannan shekarar.

Mataimakin Kwamanda mai kula da shiyya ta daya a Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), Dokta Godwin Omiko ne ya sanar da hakan lokacin da ya kai ziyarar neman hadin kai ga Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli a fadarsa da ke Zariya ranar Alhamis.

Jami’in ya lura cewa ya zuwa watan Yunin shekarar 2021, an samu mutuwar mutum 350, inda ya ce alkaluman na bana sun rubanya na bara.

Ya ce hakan ne ya sa suka kai ziyarar don neman goyon bayan masarautar kan hanyoyin rage yawan haduran.

Kwamandan shiyyar, wanda shi ne ke kula da Jihohin Kaduna da Katsina da Kano da Jigawa, ya roki hadin kan Sarkin a Jihohin don shawo kan matsalar.

“Mai Martaba, muna bukatar gudunmawar masarauta saboda yana da matukar muhimmanci wajen kiyaye matsalar a wannan yankin. Mun gudanar da tarukan wayar da kan jama’a a tashoshin mota, amma babu wani canji na ku-zo-ku-gani,” inji shi.

Godwin Omiko ya alakanta haduran da ake yawan samu da gudun wuce sa’a da kokarin wuce wasu da tukin ganganci da shaye-shaye da kuma kun bin dokokin hanya.

Da yake mayar da jawabi, Sarkin na Zazzau, Ahmed Nuhu Bamalli, ya koka da yawan haduran da ake samu, inda ya roki hukumar da kada ta gaza a yunkurin nata

Ya ba hukumar tabbacin hadin kai da goyon bayan da take bukata.