✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutumin da ya tsara taken NYSC ya rasu

Buhari ya yi ta'aziyyar rasuwar Oluwole Isaac Adetiran, wanda ya rasu yana da shekara 75

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika ta’aziyyarsa kan rasuwar mutumin da ya tsara taken Shirin Yi Wa Kasa Hidima (NYSC), Oluwole Isaac Adetiran.

A ranar Alhamis, Buhari, ta hannun hadiminsa, Femi Adesina, ya jajanta wa iyalai da abokan arzikin Oluwole Isaac Adetiran, wanda ya rasu yana da shekara 75.

Ya bayyana cewa marigayin ya bar babban abin koyi, kuma ba za a taba mantawa da shi ba, duba da yadda shirin NYSC ke ba wa matasan Najeriya kwarin gwiwa da kyakkyawan fata.

Buhari ya bukaci matasan Najeriya da su yi koyi da irin sadaukar da kan mamacin ta bangaren rayuwa da neman kusanci da Allah domin samun nasara a kowane bangare.

A lokacin rayuwarsa, Oluwole Isaac Adetiran ya samu lambar girmamawa ta kasa ta MON.

Ya kasance tsohon Shugaban Sashen Kade-kade da Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Ibadan.

Shi ne kuma Daraktan Kade-kade na Celestial Church of Christ Worldwide.