✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mutuwa mai yanke jin dadi

Kowane rai mai dandanar mutuwa ne.

Huduba ta Farko:

Godiya ta tabbata ga Allah, wanda Ya halicci sammai ba tare da wasu turaku da kuke ganinsu ba. Godiya ta tabbata ga Allah, kuma Shi ne Ma’ishi.

Tsira da Amincin Allah su kara tabbata bisa BawanSa wanda Ya zaba, Annabinmu Muhammad (SAW) da alayensa da sahabbansa da wanda ya jibince shi.

Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya hukunta mutuwa a kan bayinSa, kuma Ya kadaita da rayuwa da tabbata.

Allah Madaukaki Ya ce: “Kuma sai magagin mutuwa ya zo da gaskiya.” Kuma Allah Madaukaki Ya sake cewa: “Kowane rai mai dandanar mutuwa ne, kuma wallahi za Mu jarrabe ku da alheri da sharri a matsayin fitina, kuma gare Mu ake mayar da ku.”

Bayan haka, ku ji tsoron Allah Ya ku Musulmi matukar jin tsoronSa! Ku yi riko da igiyar Musulunci mai aminci, ku sani lallai ne Shi (Allah) Ya tserar da ku daga wuta.

Kuma lallai Mala’ikan Mutuwa ya kawar da kai ne daga gare ku ya koma ga wadansunku da sannu zai bar wadansunkun ya komo gare ku, don haka ku zauna cikin shiri!

Mai hankali shi ne wanda yake taka-tsantsan da ransa kuma yake yin aiki domin abin da yake zuwa a bayan mutuwa. Tababbe kuma shi ne wanda yake bin son zuciyarsa, kuma yake rika buraceburace a kan Allah, har mutuwa ta zo masa.

Ya ku Musulmi! Lallai mafi girman wa’azi shi ne mutuwa, Allah Ya kaddara ta a kan wanda Ya so daga cikin halittu. Komai nisan ajalin abin halitta da tsawon rayuwarsa sai mutuwa ta riske shi, ya mika wuya ga karfinta.

Allah Madaukaki Ya ce: “Kowane rai mai dandanar mutuwa ne, sannan zuwa gare Mu ake mayar da ku.” (Ankabut:59). Da Allah zai sanya dawwamma ga wani daga cikin halittunSa da ya kasance AnnabawanSa masu tsarki da ManzanninSa mukarrabai ne.

Kuma da wanda zai fi su cancantar haka shi ne zababbe daga cikin zababbunSa, wato Annabi Muhammad (SAW), amma hakan bai yiwu ba, sai ma Allah Ya shaida masa cewa: “Lallai ne kai mai mutuwa ne, kuma lallai ne su ma masu mutuwa ne.” (Zumar:30).

Mutuwa tilas ce babu makawa daga gare ta, kuma ba a guje mata, za ta riske mu a cikin gidajenmu da a kan duwatsu da a sararin sama da a karkashin ruwa.

Mala’ikun da suke cikin sama ma ba su tsere mata, haka mala’ikun da suke cikin kasa. Babu wani mutum ko aljani ko dabba da zai tsere mata, ko da ta kasancewa a cikin gidaje masu tsaro da dogayen katangu ne.

“Duk inda kuka kasance mutuwa za ta riske ku, ko da kuna cikin gidaje masu cike da tsaro.”

Da ana kubuta daga mutuwa da mutum ya ba da jikinsa da karfinsa da dukiyarsa da wadatarsa da ikonsa da mulkinsa da duk abin da ya mallaka domin ya kubuta daga gare ta! Abin ya yi girma ga mutane ba su hankalta.

Idan ba haka ba, ina Adawa da Samudawa? Ko kuma ina Fir’auna Ma’abocin Turaku? Ina Kisrori da Kaisarori (na Rum da Farisa? Ina manyan jabbarai (masu girman kai da jiji-da-kai ) masu mulki? Mutuwa ba ta jin tsoron kowa kuma ba ta barin kowa! Tana dauke jariri daga bakin nonon uwarsa. Tana auka wa matashi saurayi mai karfi da jarumtaka ta yi galaba a kansa.

Ya ku mutane! Sha’anin mutuwa a bayyane yake kuma a fili. Gurbinta sirri ne daga cikin asirai wadanda suke zama abin lura ga masu hankali.

Tana girgizawa tare da shan kan hankulan mutane, tana barin masana falsafa da likitoci suna ta kai-kawo cikin rudu ba su gano sirrinta ba.

Tsayawa bincike a kan mutuwa bata ne mabayyani da bala’i mai girma! Babu mai mantawa da ita face ya yi dagawa, babu mai gafala daga gare ta, face tababbe, kuma ita ba ta da magani.

Ba a kauce mata, sai dai mutum ya rika tuna fadin Allah Madaukaki: “Rai bai san abin da zai aikata gobe ba, kuma bai san a wace kasa zai mutu ba. Lallai ne Allah Masani ne Mai ba da labari.” (Lukman:30).

Huduba ta Biyu:

Ya ku Musulmi! Ya kamata kowane Musulmi ya rika tuna wasu darare biyu, daren da yake zaune a gidansa tare da iyalinsa da ’ya’yansa yana mai jin dadi da lafiya, yana mai annashuwa tare da ’ya’yansa yana yi musu wasanni suna yi masa wasanni da kuma daren da yake bin wannan, lokaci da mutum yake cikin wannan jin dadi, yake jin dadin lafiyarsa, yake ni’imtuwa da ni’imar lafiya, yana ji da karfi da samartakarsa ko dukiyarsa, kwatsam sai mutuwa ta zo masa, ta tafi da shi ba tare da ya shirya ba! Kan haka ne Manzon Allah (SAW) ya ce: “Ku yawaita tuna mai rusa jin dadi (mutuwa).”

Ya ku Musulmi! Lallai muna da abin koyi mai kyau daga rayuwar magabatan kwarai, abin koyi mai dadi. Hakika sun kasance suna yawaita tuna mutuwa hatta a lokacin wadata da yalwa da jin dadi. Wannan yana dada karfafa su ga dada yin da’a ga Allah da guje wa saba maSa.

Wadansu mutane sun ce: “Mun shiga wurin Adda’us Sulamiy (Rahimahullah) domin mu gaisar da shi a kan rashin lafiyar da ya rasu a cikinsa, sai muka ce masa: Yaya jiki? Sai ya ce: “Mutuwa ta zo min har wuya, ga kabari a gabana, kuma Kiyama ce wurin tsayuwana, gadar Jahannama ce kawai ta saura ban san me za a aikata da ni a kanta ba!” Sannan ya yi kuka, kuka mai tsanani har ya suma.

Da ya farka sai ya ce: “Ya Ubangiji! Ka yi min rahama, Ka sassauta min kan abin da nake tsoro a kabari da kuma tafiyata zuwa ga mutuwa. Kuma Ka yi min rahama a yayin tsayuwata a gaba gare Ka, ya Mafi rahamar masu rahama!”

Almaziniyyu ya shiga wurin Imam Shafi’i lokacin yana jinyar da bai tashi ba, sai ya ce masa: “Yaya jiki ya Abu Abdullahi?” Sai ya ce: “Na wayi gari Dinari bai da amfani, na wayi gari mai rabuwa da ’yan uwana, mai haduwa da mugun aikina, mutuwa tana kaina da takubbanta, kuma ina mai bijirowa ga Ubangijina Madaukaki. Kuma ban sani ba, shin ruhina zai wuce ne zuwa ga Aljanna, in yi masa murna, ko kuwa zuwa ga wuta in yi masa jaje!”

To, yakai rai, mai bin dadin son zuciya! Ka bar dadin wannan tunani na sa’a daya, ana tunatar da kai cewa lallai jin dadin gajere ne, ukuba kuma mai tsawo ce. Abin mamaki! Mai jin dadi yana sayen sha’awa ta sa’a daya cikin wahala da damuwa. Sabon sa’a daya amma mutum zai yi nadamar da bai yi ba, da yawa rai zai kaskanta a bayansa!

Da yawa rai kan yi tsatsa saboda shi! Hawaye ya zuba saboda tuna shi! Allah Ya yi mana tsari gaba daya daga gafala da mummunar makoma a cikin dukiya da iyali da ’ya’ya.

Ya bayin Allah! Ina fadin abin da kuke ji, ina neman gafarar Allah a gare ni da ku da sauran Musulmi daga dukkan zunubi, ku nemi gafararSa, lallai ne Shi Mai gafara ne, Mai jinkai.

Hudubar Imam Muhammad Awwal Isa Umar, Masallacin Juma’a na Khalid Bin Walid, Awalah, Bauchi wacce Salihu Makera ya Fassara