✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Na amince zan dambata da Tyson Fury —Dillian Whyte

Fury ya bayyana cewa Whyte ba sa’an dambatawarsa ba ne.

Dillian Whyte ya rattaba hannu kan yarjejeniyar fafatawa da zakaran ajin masu nauyi na Damben WBC Tyson Fury sa’o’i kafin cikar wa’adi.

Whyte, mai rike da kambin WBC na wucin gadi, zai kalubalanci Fury wanda shi ne zakaran WBC ajin nauyi, wanda ya doke Alexander Povetkin don samun kambunsa na yanzu.

Whyte ya ce a shirye yake ya tambata da Fury a duk filin da yake bukata da kuma lokacin da ya ga dama, saboda ya dade yana jira.

A nasa bangaren, Fury ya bayyana fafatawar a matsayin mafi sauki saboda Whyte ba sa’an dambatawarsa ba ne.

Ana sa ran ayi gumuzun a ranar 23 ga watan Afrilu, mai yiwuwa a filin wasa na Wembley.