✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Na kusa kashe kaina a kan rashin kudin makaranta’

Mahaifina da lakcarori sun sa ni a tsaka mai wuya.

Saura kiris wani matashi ya kashe kansa saboda rashin kudin makaranta na shekara biyu a lokacin da yake tsaka da karatu a jami’a.

Matashin da aka sakaya sunansa, ya shaida wa Aminiya cewa ya fara karatunsa na jami’a cikin wadata, daga baya abubuwa suka sauya wa mahaifinsa, ta kai ga an kasa biyan kudin makarantarsa, lamarin da ya ci gaba har ta kai ga duniya ta yi masa kunci, ya fara tunanin rayuwarsa ba ta da amfani.

Ya shaida wa shirin ‘Najeriya A Yau’ — wanda Aminiya ke gabatarwa a intanet — cewa ya yi duk iya kokarin da zai kai ga kammala karatunsa, amma wasu lakcarori da ma’aikatan jami’ar suka kara dagula masa lissafi.

Ya ce bayan ya yi ta fadi-tashi domin ya hada kudin makaranta, ga shi lokaci ya kusa kurewa, ana dab da fara jarabwa, sai ya nemi a jinkirta masa zangon karatun (deferring).

Amma kuma sai lakcarorin da jami’an da ke da alhakin yin hakan, kowanne ya rika yi masa wasa da hankali har lokaci ya kure, ba yadda zai yi, sai dai ya tattara ya koma gida.

Bayan dawowarsa gida kuma rayuwa ta kara yi masa dabaibayi, ga shi takwarorinsa sun yi masa nisa, wasu ma har sun kammala karatunsu sun fara aiki, shi kuma al’amuransa ba su dawo daidai ba.

Ga tattaunawar da Muhammad Auwal Suleiman ya yi da shi, a shirin da ya mayar da hankali kan Ranar Wayar Da Kai kan Nisantar Kashe Kai ta Duniya, da ake yi a kowace ranar 10 ga watan Satumba.

“A 2016 na samu gurbin karatu a Jami’a… Shekarata ta farko lafiya lau, Alhamdulillah na gama, zuwa [shekara] ta biyu sai na samu matsala, daga tallafi na iyaye — kudin makaranta.

“Babu yadda ban yi ba in samu in biya, [amma] ban [samu na] biya shi ba.

– Na shiga tsaka mai wuya

“To a lokacin sai kanwata ta hada min kudi ta sa babana ya tura min, saboda dab da jarabawa ne lokacin.

“Sai shi kuma ko ya aka yi, ya yi amfani da kudin …bai tura min ba. Haka dai har aka fara jarabawa ban samu na biya ba; Ni kuma sai na yi maganar ‘deferring’.

“Ina fadi-tashin yadda zan yi ‘deferring’ din, shi ma ya zo yana so ya gagara; Duk lakcaran da na samu sai ya kawo min wasu kabli da ba’adi, karshenta ma dai Sakataren Ilimin na yi kusan wata daya ina bin shi.

“Har na gaji ma dai na koma gida, don lokacin ma ina fama da abin da zan ci.

– Rayuwata babu amfani

“Sai na ga lokacin ga duka tsararrakina yawanci sun gama makaranta, yawancinsu suna wani aiki…tunani dai da yawa kawai!

“Na kusan wata daya ba na ko kallon inda babana yake saboda haushi…kan wannan abin da ya yi.

“Kuma lokacin minti daya-biyu in na kalli mahaifiyata sai in ga tana kuka kan abin da ta san yana damu na…saboda ko abu na damu na ban iya fitowa fili in nuna wa mutum.

“Nakan kullle kaina a daki in yi kuka, har dai ‘deferring’ bai zo ya yiwu ba, har shekara ta juyo, kawai na yi tunanin ban ma da wani amfani [a] rayuwa,” inji shi.

Dalilin fasa kashe kaina

Matashin ya ce halin da ya shiga ya yi tsanani har ya fara tunanin ya kashe kansa.

To amma da Allah Ya kaddara yana da sauran kwana, sai wani abin ya taba zuciyarsa, “Na duba na ga mahaifiyata, sannan yaro ne ni, ina da sauran tafiya a rayuwata, kuma akwai mutane da yawa suna nan da ba su yi makaranta ba kuma sun dace a rayuwa, sai na bude wani babi.”

A cewarsa, “Sai na duba na ga mahaifiyata, kai! Bai kamata in bar ta a cikin wani hali ba; Ya zamo ma ni ne na koma ina ba ta hakuri saboda kar ta damu da abin da ke damu na.”

Ya ce daga baya, “Alhamdulillahi yanzu ga shi na yi rajista ina [karatu] a kwalejin kimiyya da kere-kere kuma ina da aikin hannuna, yanzu ko me ya taso ni da kaina zan iya biya wa kaina bukata.

– Kira ga masu son su kashe kansu

Ya shawarci mutane, musamman matasa da su daina tunanin kashe kansu.

A cewarsa, maimakon haka su rika duba al’umma da kuma amfanin da za su iya yi a nan gaba a rayuwa, “Don mutum ya rasa wani abu, hakan ba ya nufin rayuwarsa ta zo karshe.”

Ya ce abin da ya faru da shi a baya ya zama masa darasi da kuma alheri, “Tun da yanzu gaskiya dai ko da a ce ban yi makaranta ba, ina da abin da zan dogara da shi, tunda yanzu haka ina daga cikin masu taimaka wa mahaifina.

“In da lokacin da yake da shi ne zai iya ba ni. Ni ma abin da na yi tunani [shi ne] lokacin da yake da shi.

“A shekarata ta farko [a jami’a] kudin da ya ba ni sun fi a kirga kuma na kashe su ta [hanyar] banza; Amma sai yanayi ya zo da yanzu shi ba shi da shi.”