Na yi ‘nadamar rera “Yau Najeriya riko sai mai gaskiya” – Mawakin Buhari | Aminiya

Na yi ‘nadamar rera “Yau Najeriya riko sai mai gaskiya” – Mawakin Buhari

    .

“Yau Najeriya riko sai mai gaskiya…” waka ce da ta taka rawa wajen tallata Shugaban Kasa Muhammadu Buhari tun lokacin da ya fara takara.

Sai dai kuma mawakin da ya rera wakar, Ibrahim Yala, ya ce yana shirin rera wata don bai wa ’yan Najeriya hakuri bisa rashin tabbatar alkawarin da ya yi musu na kyautatuwar rayuwarsu idan Buhari ya zama shugaban kasa.

Ya bayyana dalilan da suka sa a wannan hirar da Aminiya ta yi da shi.