✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Naira miliyan 19 muke biyan kocin Eagles duk wata – NFF

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya sanar da manema labarai a Litinin da ta gabata cewa rade-radin da ake  bazawa…

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) Mista Amaju Pinnick ya sanar da manema labarai a Litinin da ta gabata cewa rade-radin da ake  bazawa cewa ana biyan kocin Super Eagles Gernot Rohr Dala dubu 60 (kwatankwacin Naira miliyan 21 da dubu 660) a matsayin albashi duk wata ba gaskiya ba ce.  Ya ce Hukumar NFF  tana biyan kocin Dala dubu 55 ne (kwatankwacin Naira Miliyan 19 da dubu 855) a kowane wata.

Shugaban ya ce, kwanan ne ma aka kara wa kocin Dala dubu 10 a kan Dala dubu 45 da ake biyansa a baya.

Shugaban ya shaida wa manema labarai haka ne a ofishinsa da ke Abuja don ya kawo karshen cece-ku-cen da ake yi game da ainihin albashin da kocin yake karba duk wata. “Ina mai sanar da ku albashin kocin Super Eagles, Rohr Dala dubu 55 ne ba Dala dubu 60 ba,” inji Pinnick.

Gernot Rohr, dan kasar Jamus da aka haifa a Faransa, kimanin shekara biyu ke nan yake horar da kungiyar Super Eagles bayan NFF ta ba shi kwanatargi. Shi ya jagoranci kungiyar Super Eagles a gasar cin Kofin Duniya da aka yi a Rasha a bara, sannan ana sa ran shi ne zai jagoranci kungiyar a gasar cin Kofin Afirka da za a yi a watan Yunin bana a kasar Masar.

Masoya kwallon kafa a ciki da wajen Najeriya da dama suna ta korafi a kan yawan albashin da ake ba kocin duk da mawuyacin halin da kasar nan ke fama da shi na rashin kudi, ganin yadda Gwamnatin Tarayya take turka-turka da ’yan Kwadago kan amincewa da mafi karancin albashi na Naira dubu 30.