NAJERIYA A YAU: Manyan Dalilan da Suka Sa aka zabi Abdullahi Adamu Shugaban APC | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Manyan Dalilan da Suka Sa aka zabi Abdullahi Adamu Shugaban APC

    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

Zaben tsohon gwamnan Jihar Nasarawa, Sanata Abdullahi Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ya bar tambayoyi da yawa a cikin zukatan jama’a.

Ganin cewa Abdullahi Adamu na daya daga cikin wadanda su ka kafa jam’iyyar PDP, ya yi gwamna sau biyu a karkashin inuwar  PDP, ya taba zama sakataren kwamitin amintattu a PDP.

Wadanne dalilai ne suka sa har shugaba Buhari ya amince da nadin Abdullahi Adamu a matsayin jagora?