NAJERIYA A YAU: Dalilin Ruguguwar Jama’a Zuwa Yankar Katin Zabe | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Dalilin Ruguguwar Jama’a Zuwa Yankar Katin Zabe

Katinan zabe
Katinan zabe
    Halima Djimrao da Muhammad Auwal Suleiman

Domin sauke shirin latsa nan

A daidai lokacin da ya rage mako biyu hukumar zabe ta Najeriya (INEC) ta rufe yin rajistar masu niyyar kada kuri’a a babban zabe da za a gudanar nan da wata takwas masu zuwa, jama’a na ta rububin zuwa a yi musu rajista.

Wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta ya nuna yadda wani fasto yana hana duk wanda bai zo da katin zabe ba shiga cocin da yake jagoranta.

Ko me ya sai a kurarren lokaci mutane ke farga?

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokacin ya tattauna da masu niyyan kada kuri’a a zaben 2023 da kuma bayanin ainihin ranar da za a rufe yin rajistar daga bakin hukumar zabe ta INEC.