NAJERIYA A YAU: Gudunmawar da kowa zai bayar wurin kawar da ta’addanci | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Gudunmawar da kowa zai bayar wurin kawar da ta’addanci

Wasu ‘yan banga da mafarauta. (Toshuwar ajiya).
Wasu ‘yan banga da mafarauta. (Toshuwar ajiya).
    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao

Domin sauke shirin latsa nan

Zuwa yanzu, ya fara zama zahiri a idon duniya cewa Najeriya ta fada cikin taskun ta ta’addanci da kullum yake mata barazana kan yiwuwar ci gaba da kasancewar ta kasa daya dunkulalliya mai shugabancin da ake yi wa biyayya.

Tuni dai kasar ta ayyana kungiyoyin ’yan bindiga guda biyar a matsayin na ta’addanci. Hudu daga cikinsu a Arewacin kasar suke, daya kuma a Kudancinta.

To ko ta wadanne hanyoyi ’yan kasar za su hada kai da gwamnati domin ceto kansu da kasar su?

Ayi sauraro lafiya.