NAJERIYA A YAU: Inda Dalar Shinkafar Najeriya Ta Yi Aure Ta Tare | Aminiya

NAJERIYA A YAU: Inda Dalar Shinkafar Najeriya Ta Yi Aure Ta Tare

Dalar Shinkafar da Shugaba Muhammadu Buhari ya Kaddamar
Dalar Shinkafar da Shugaba Muhammadu Buhari ya Kaddamar
    Muhammad Auwal Suleiman da Halima Djimrao

 

Domin sauke shirin latsa nan

Kusan wata biyar ke nan cif tun bayan da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da Dalar Shinkafa a kusa da babban filin jiragen sama na Nmadi Azikwei da ke Abuja.

Wannan lamari dai ya ja hankalin jama’a, musamman ma jin cewa buhun shinkafa miliyan daya da dubu dari biyu ne aka yi wannan dala da su.

An ce an yi hakan ne da zimmar kawo karshen tashin gwauron zabon da farashin shinkafar ke yi, amma har yanzu ‘yan kasar sun ce ba su gani a kasa ba.

Shin ina wannan Dalar Shinkafa ta yi aure ta tare?