Najeriya A Yau: Yadda Tsaro Da Tattalin Arziki Za Su Shafi Zaben 2023 | Aminiya

Najeriya A Yau: Yadda Tsaro Da Tattalin Arziki Za Su Shafi Zaben 2023

    Muhammad Auwal Suleiman da Bilkisu Ahmed da Halima Djimrao

Domin sauke shirin latsa nan

Yanayin tsaro da tattalin arziki na taka muhimmiyar rawa a wuring gudanar da zabe wanda kuma babban jigone wajen tabbatar da dorewar tsarin Dimokuradiyya.

 

Taron tattaunawa na shekara-shekara da kamfanin Media Trust mai buga jaridar Daily Trust na wannan karon ya mayar da hankali ne a kan rawar da yanayin tsaro da tattalin arzikin Najeriya za su taka wurin juya akalar zaben kasar na shekarar 2023.

 

Shirin Najeriya A Yau na wannan lokaci ya tattaro bayanan masana akan harkokin tsaro, tattalin arziki da tsaro.