✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Najeriya ta karbi rigakafin COVID-19 daga Rasha

Gwamnatin Najeriya ta karbi samfarin rigakafin allurar rigakafin cutar coronavirus daga kasar Rasha. Kafar watsa labarai ta Channels ta rawaito cewa Ambasadan Rasha a Najeriya,…

Gwamnatin Najeriya ta karbi samfarin rigakafin allurar rigakafin cutar coronavirus daga kasar Rasha.

Kafar watsa labarai ta Channels ta rawaito cewa Ambasadan Rasha a Najeriya, Alexey Shebarshin shi ya mika samfurin ga Ministan Lafiya Dokta Osagie Ehanire, a lokacin da ya kai ziyara ma’aikatar ranar Juma’a a Abuja.

Ambasadan ya kuma mika taimakon wasu kundin bayanai da za su taimaka wa Najeriya a kan rigakafin na COVID-19 ta yadda za ta fadada bincike.

“Mun dukufa wajen tattara bayanan ilimi domin samar da kayan aikin da su taimaka wajen jinya da kuma samar da alluran rigakafi.

“Mun bayyana sha’awarmu a kan rigakafin cutar COVID-19 don mu samu damar fadada bincike ta yadda za mu yi aiki kafada da fafada”, inji ministan.

Ya ce, Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashe da suke fadada musayar binciken ilimi da hukumomi da kuma kasashe da dama domin dakile yaduwar cutar.

Ehanire ya yaba wa Ofishin Jakadancin Rasha a Najeriya bisa yadda ya bawa Najeriya damar mallakar samfurin rigakafin, lokaci kadan bayan Gwamnatin Rasha ta fitar da bayanin samar da ragakafin