✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barnar da rashin shugabanci nagari ya yi wa Najeriya a shekaru 63

Har yanzu ba a makara ba wajen gyara kura-kuran da suka dabaibaye Najeriya suka jefa ta hanlin da take ciki yanzu

Alhamdulillah ala kulli halin! Alhamdulillah! Duk abin da ake nema a kasa na arziki da wadata Allah Ya Yi mana a Najeriya, shugabanci kawai muka rasa.

Don haka, a ganina, wannan kalma ta godiya, ita ce mafi cancanta da ta kamata kowane dan kasa ya fadi a irin wannan lokaci na zagayowar ranar da kasar nan ta samu ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka na kasar Birtaniya, wato 1 ga watan Oktoban 1960, wadda yau Lahadi muka shekara 63, daidai da kai wannan matsayi.

Abin da ya sa na bude da godiya ga Allah (SWT), bai wuce irin yadda na san wasu daga cikin matsalolin da kasar nan ta ratso a cikin wannan lokaci na zamanta kasa daya mai ’yancin kanta da kuma irin yadda cikin taimakon Allah muka wuce su, kuma muna nan zaune, a matsayin kasa daya dunkulalliya.

Rigingimin da suka yi wa Najeriya tarnaki

Duniya ta san cewa har Yakin Basasa muka yi na tsawon wata talatin, amma cikin ikon Allah muka ga karshensa, yau shekara 53.

Bayan kammala Yakin Basasar ne, wanda dama can batun kabilanci da hadamar mulki ya haddasa shi, sai kuma rigingimu masu kama da na addini da kabilanci, kamar fadan Fulani makiyaya da manoma da fadan kabilanci da ake ta fama da shi suke kuma neman samun gindin zama a jihohi irin su Kaduna da Filato da Taraba da sauran sassan kasar nan.

Yau shekara goma sha hudu ke nan rikicin Boko Haram ya bulla a Jihar Borno, wanda sannu a hankali ya yi ta yaduwa har sai da ya game jihohin Arewa maso Gabas, sannan ya game kasa, har ya bullo kasashen makwabta irin su Jamhuriyyar Nijar da Chadi da Kamaru da Ghana, har yanzu kuma ana fama da shi.

Ana cikin rikicin Boko Haram, sai ga bullar masu satar shanu, wadanda su ne suka rikide suka koma ’yan bindiga ko ’yan fashin daji, masu yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa, annobar da ita ma ta game kasa har ta fada kasashen makwabta.

A Kudu maso Gabas ’yan haramtacciyar kungiyar Neman Kafa kasar Biyafara, kasar da suka nemi su kafa a 1967, aka yake su wato IPOB, a ’yan shekarun nan suna ta kara kada kugen sai sun tabbatar da hakan, musamman a shiyyarsu ta ’yan kabilar Ibo. Suna kuma cin karensu ba babbaka, wajen kai harehare da kashe jami’an tsaro da farar hula, baya ga hana tafiyar da harkokin yau da kullum inda suke ba da odar a zauna gida.

Sauran ayyukan ta’addanci irin su fashi da makami da na kungiyoyin matsafa da kisan gilla masu kama da hamayyar siyasa suna neman su zama ruwan dare a kasa. Haka batun yake a kan satar danyen man fetur da fasa butututn man kullum sai kara ta’azzara suke a yankin Neja-Delta mai arzikin man fetur.

Ko a kwanan nan an ji Mashawarci kan Harkokin Tsaron kasa Alhaji Nuhu Ribadu a yayin wata ziyara da ya kai yakunan da ake hakar man fetur a jihohin Abiya da Ribas yana cewa a kullum kasar nan na asarar gangar danyen man fetur dubu 400, daga ta’asar masu sata da fasa bututun man fetur.

Annobar rashin kishin kasa

Cin hanci da rashawa tsakanin jami’an gwamnati ya zama ado ta yadda a kullum kara daukar sabon salo yake. Annobar rashin kishin kasa da rashin yarda da juna sai kara samun gindin zama suke a kasar nan. Alhali ba a kan irin wannan mummunan tsari Turawan mulkin mallaka suka mika mulkin kasar nan ga shugabannin farar hula na farko ba, irinsu Shugaban kasa Dokta Nnamdi Azikwe da Firayi Minita Sa Abubakar Tafawa balewa da Firimiyan Jihar arewa na farko Sa Ahmadu Bello Sardaunan Sakkwato da Cif Obafemi Awolowo Firimiyan Jihar Yamma da Cif Macheal Okpara Firimiyan Jihar gabas.

Sanin kowa ne cewa wadancan shugabannin farko sun jajirce wajen ganin lardunansu sun ci gaba, mutanensu kuma sun zama mutane, ta hanyar tallafar dukkan bukatun da za su taimaka masu a rayuwarsu.

Alal misali mu a nan Arewa, gwamnatin Sa Ahmadu Bello ita ta gina masana’antu, musamman masaku a Kaduna Hedikwatar Arewa baki daya da gidan rediyo da talabijin a Kaduna da Jami’ar Ahmadu Bello a Zariya da Makarantar Ayyukan Gona ta Kabba a Jihar Kogi ta yau, baya ga matsakaitun makarantun gaba da sakandare dabandaban.

A lokacin su Sardauna Arewa kawai ake magana, ba wani batun a je garin Sardauna ko wani ministansa ko babban sakatare a gina masa wani abu, sai inda ya cancanta. Shi ya sa kullum ake maganar irin nasarorin da suka samu wajen yi wa Arewa aiki da hada kan jama’arta.

Rashin shugabanci nagari

Sabanin a yau da komai za a yi na ci gaban jama’a, ba don jama’a ake ba sai don Shugaban kasa ko Gwamna ko wani dan majalisa ko shugaban karamar hukuma.

Ba dai batun cancanta kusan a kan komai za a yi a yau, sai don wane ko wa ka sani ko da kuwa hukunci ne a kotun alkali.

Rabuwar kai

A zaman ’yan marina kasar nan take a yau, kowa da inda ya sa gabansa, batun kabilanci da addini da jinsi su kadai suke tasiri. A gefe daya kuma shugabanni na ta kururuwar a hada kai, don ci gaban kasa amma a duk lokacin da za su yi wani abu na kasa, sai ka ga sun karkata ga kabilarsu ko addininsu.

Alal misali ko a makon jiya lokacin da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yake ganawa da wasu ’yan kasar nan mazauna kasar Amurka a birnin Washington DC, a cikin jawabinsa ya ce kasar nan kasa daya ce kuma al’umma daya. Amma kuma a nan gida ana ta sukarsa a kan akasarin nade-naden hadiman gwamnatinsa da ya yi zuwa yanzu ya fi karkata ga ’yan kabilarshi ta Yarbawa.

A ra’ayina, har yanzu ba a makara ba wajen gyara kura-kuran rashin adalci da son kai da rashin kishi da rashin kaunar juna da makamantan miyagun halaye na cin hanci da rashawa da suka dabaibaye mu.

Yanzu kuma ya kamata kowa ya daura damara, wajen yin abin da ya dace. Allah sai Ya taimake mu. Duk abin da ake nema a kasa na arziki da wadata Allah Ya Yi mana, shugabanci kawai muka rasa.

Barka da zagayowar Ranar ’Yanci kai. Allah Ya maimaita mana cikin koshin lafiya da zaman lafiya da karuwar arziki da son junanmu. Amin summa amin