✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NDLEA ta kama hodar Iblis ta N2bn a lokaci guda

Hukumar ta kama sunduki biyu cike da hodar Iblis da kudinta ya kai Naira biliyan biyu a lokaci guda.

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta kama hodar Iblis cikin sunduki biyu da kudinta ya kai Naira biliyan biyu a lokaci guda.

Hodar Iblis din da aka makare sunduki biyu da ita, nauyinta ya kai kilogram 40,230, kuma an shigo da su tashar jiragen ruwa ta Apapa ne da ke Legas, daga Indiya.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce, “Miyagun kwayoyin da muka kama a ranar 8 ga Fabrairu 2022 sun shigo ne a cikin sundukai biyu; Sunduki na farko yana dauke da kwali 1,125 na miyagun kwayoyin, na biyun kuma an sanya kwali 1,751 wanda kudinsu ya kai N2,012,500, 000”.

Babafemi ya ce NDLEA ta kama hodar Iblis ne da taimakon hukumar tsaro ta DSS, sojan ruwa da kuma kwastam tare da takwarorinsu na kasashen waje da suka taimaka da bayanai.

Kamen da hukumar ta yi na zuwa ne kimamin mako guda bayan ta kama kwayar kodin da nauyinta ya kai kilogiram 14,080.

Shugaban hukumar, Birgediya Mohammed Buba Marwa (ritaya), ya jinjina wa jami’an hukumar kan namijin kokarin da suka yi na kama miyagun kwayoyin.

Ya kuma bayyana godiya bisa taimakon da sauran hukumomin tsaro da takwarorinsu na kasashen waje suke musu.

Buba Marwa ya bayyana shirinsu na karya lagon masu safarar miyagun kwayoyi zuwa Najeriya ko suke wuce da ita ta kasar a tsawon wannan shekarar.