✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

NDLEA ta lalata tan 24 na miyagun kwayoyi a Kwara

Kwamandan NDLEA a jihar, Ibrahim Saidu, ya ce, sun gurfanar da dillalan miyagun kwayoyi su 171 a Jihar Kwara a cikin wannan shekara.

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA), ta lalata miyagun kwayoyi da nauyinsu ya kai tan 24.6 da ta kama a Jihar Kwara.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN), ya ce, a ranar Laraba NDLEA ta yi wannan aikin ne a Ilorin.

Gwamnan jihar, AbdulRahman AbdulRazaq, ya yaba wa hukumar da wannan nasarar da ta samu a jihar.

AbdulRazaq ya bai wa NDLEA tabbacin gwamnatinsa za ta ci gaba da mara mata baya don ci gaba da aikinta a jihar yadda ya kamata.

A nasa bangaren, Kwamandan NDLEA a jihar, Ibrahim Saidu, ya ce, sun samu nasarar gurfanar da dillalan miyagun kwayoyi su 171 a jihar a cikin wannan shekara.

(NAN)