NDLEA za ta yi wa ’yan takarar APC gwajin shan miyagun kwayoyi | Aminiya

NDLEA za ta yi wa ’yan takarar APC gwajin shan miyagun kwayoyi

    Abbas Jimoh da Abubakar Muhammad Usman

Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa (NDLEA) ta aike wa Shugaban APC na Kasa, Sanata Abdullahi Adamu, takardar neman yi wa ’yan takarar jam’iyyar gwajin shan miyagun kwayoyi.

Shugaban NDLEA, Muhammad Buba Marwa ne ya bayyana haka ranar Laraba a Abuja, yayin da ya ke jawabi a wajen wan bikin karramawa kashin farko na hukumar.

“Yin gwajin shan miyagun kwayoyin ya zama dole don tabbatar da cewa ’yan siyasar da aka bai wa muhimman ofisoshi ba su yi amfani da kudin kasa wajen sayen hodar iblis ko miyagun kwayoyi ba maimakon samar da ayyukan da ake bukata ga talakawa,” a cewar Buba Marwa.

Ya bayyana cewa idan lokacin gudanar da zaben fitar da ’yan takarar jam’iyyar PDP da sauran jam’iyyu ya yi, hukumarsa za ta aike wa shugabanninsu a rubuce bukatar yi wa ’yan takararsu gwajin shan miyagun kwayoyi.

Bayanin nasa na zuwa ne bayan a ranar Talata APC ta fara sayar da takardun neman tsayawa takara a zaben 2022 ga mambobinta.

Tun a makon jiya ne APC ta shiga bakin duniya bayan ta fitar da sanarwar kudin fom takara, wanda hatta wasu daga cikin masu neman tsayawa takara suka koka game da tsananin tsadar takardun.

Wasu na ganin kudin da aka zabga wa fom din takarar wata hanya ce ta hana matasa shiga a dama da su a jam’iyyar.

Wasu kuma na ganin hakan zai bude kofar yin satar kudin kasa ga duk wanda ya samu damar darewa wata kujerar siyasa, don ganin ya mayar da abin da ya kashe wajen yin takara.