✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NECO ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandare ta 2022

Hukumar ta ce a bana yawan daliban da suka ci jarabawar bai kai na bara ba

Hukumar da ke Shirya Jarabawa ta Kasa (NECO) ta saki sakamakon jarabawar kammala sakandare da aka yi a watan Yulin 2022 a fadin Najeriya.

Shugaban hukumar, Farfesa Danladi Wushishi ne bayyana hakan a Minna, babban birnin jihar Neja, a ranar Alhamis.

A cewarsa, daga cikin dalibai 1,209,703, da suka zauna jarabawar a bana, kaso 60.74, wato dalibai 727,864 ne suka samu akalla darussa biyar, ciki har da Turanci da Lissafi.

Ya ce idan aka kwatanta da sakamakon 2021 inda dalibai 878,925 (kaso 71.64 cikin 100) da suka samu turancin da Laissafi, a bana an sami raguwar kaso 10.9 ke nan.

Shugaban na NECO ya ce an saki sakamakon ne kwana 45 bayan kammala jarrabawar, inda ya ce daga ciki kuma dalibai 1,031 ne masu bukata ta musamman, 98 kuma zabiya, 177 suna da larurar in’ina, sai kuma masu matsalar ji kimanin 574 da kuma makafi 107.

Kazalika, ya ce daga cikin daliban da suka zana jarabawar, guda 630,180, wato kaso 52.58 cikin 100 maza ne, sai kuma dalibai 568,232 wato kaso 47.41 da suka kasance mata.

Ya kuma ce, “Daliban kuma da aka kama sun yi magudi yayin jarrabawar sun kai 13,594, wato kaso 0.13, sabanin guda 20,003, wato kaso 1.63 da aka samu a bara,” inji Farfesa Wushishi.

Shugaban na NECO ya ce hukumarsa ta shahara wajen rashin daga kafa kan kowanne nau’i na magudin jarabawa, wanda a cewarsa hakan ne ma ya sa aka samu raguwar masu magudin a bana, in aka kwatanta da alkaluman bara.

Sai dai ya ce an kuma bayar da shawarar soke rajistar makarantu hudu daga ci gaba shirya jarrabawar a nan gaba saboda samun su da aikata magudi.