✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Nigeria Air: Ko sisi ba mu kashe ba wajen dauko hayar jirgin Habasha – Sirika

Ya ce babu kamshin gaskiya a labaran da ake yadawa kan kashe makuden kudade

Tsohon Ministan Sufuri, Hadi Sirika, ya ce ko sisi ba su kashe ba wajen dauko hayar jirgin kamfanin Ethiopian Airlines na kasar Habasha, wanda aka yi amfani da shi wajen kaddamar da jirgin Nigerian Air.

Aminiya ta rawaito muku yadda Gwamnatin Tarayya ta ce ta dauko hayar jirgin samfurin Boeing 737-800, mallakin kasar ta Habasha, ana dab da tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya mika mulki.

Daga bisani dai Shugaban kamfanin na Nigeria Air da kansa ya amsa cewa hayar jirgin suka dauko domin kaddamarwar, inda mutane suka yi ta sukar yadda aka kashe kudade wajen dauko hayar.

To sai dai yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise ranar Lahadi, tsohon Ministan ya karyata zargin da aka yi cewa sun kashe kudin wajen dauko hayar.

Ya kuma ce tun shekara ta 2016 da aka fara shirye-shiryen kaddamar da jirgin, Naira biliyan biyar kawai aka ware wa shirin.

Sai dai ya ce duk da haka, biliyan uku kawai aka fitar daga cikin adadin, wanda ya kunshi komai, ciki har da na bayar da shawarwari da samun lasisi da samar da ofishi da kuma biyan albashin ma’aikata.

Hadi Sirika ya kuma ce babu kamshin gaskiya a labarin da ake yadawa a cewa an kashe Naira biliyan 85 wajen shirin.