✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

NSCDC ta kama matashi kan zargin kona gidaje 4 a Gombe

Matashin ya cinna wa gidajen wuta ne sanadiyyar wani sabani da ya shiga tsakaninsa da wani yayansa.

Hukumar Tsaro ta Cibil Difens ta kama wani matashi mai suna Segun Bulus kan zargin kona wasu gidaje guda 4 a garin Dele Jesus da ke Karamar Hukumar Balanga ta Jihar Gombe.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, matashin mai shekaru 27 ya yi wannan aika-aikar ce a daren Talata wayerwar gari Laraba.

Da yake tabbatar da lamarin, Kwamandan hukumar, Muhammad Bello Mu’azu, ya bayyana cewa sun kama matashin ne bayan an soma hatsaniya tsakaninsa da magidanta da ya haddasawa rasa matsugunni.

Hotunan gidajen da matashin ya kona

Kwamanda Mu’azu ya yi karin da cewa tun farko dai matashin ya cinna wa gidajen wuta ne sanadiyyar wani sabani da ya shiga tsakaninsa da wani yayansa.

Kwamandan ya ce suna ci gaba da gudanar da bincike kuma da zarar sun kammala za su tura wanda ake zargin kotu.