✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Oshiomhole ya fito takarar shugaban kasa

Oshiomhole ya ce zai yi wa masu kudi karin haraji kuma zai kawo karshen yajin aikin ASUU

Tsohon Shugaban Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole, ya shiga jerin masu neman kujerar shugaban kasa a zaben 2023.

Oshiomhole, wanda tsohon Gwamnan Jihar Edo ne ya sanar da fitowarsa takarar shugaban kasa ne a lokacin da yake jawabi ga magoya bayansa a Abuja ranar Laraba.

“Ba zuwa na yi domin korafi kan gazawarmu ba, fitowa na yi domin tattaunawa kan abin da nake da yakinin cewa ya dace mu yi na daban domin dora Najeriya a kan turbar cigaba da bunkasa,” inji Oshiomhole.

Ya yi alkawarin idan ya zama shugaban kasa zai yi duk mai yiwuwa don kawo karshen yajin aikin malaman jami’a da kuma yi wa Najeriya gyara ta samu cigaba mai dorewa.

Ya kara da cewa idan ya zama shugaban kasa, zai mayar da hankali wajen farfado da tattalin arziki da burin mutanen Najeriya, da kuma tsarin da za a yi wa masu kudi karin haraji.

Da yake jawabi a Cibiyar Rayar Adabi da Al’adu ta Cyprian Ekwensi da ke Abuja, tsohon shugaban APC na kasar ya ce yawan yajin aikin malaman jami’a babban abin damuwa ne ga dalibai da iyayensu.

“Ina so in yi duk mai yiwuwa wajen tattaunawa da ASUU da sauran masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi domin tabbatar da ganin jadawalin karatu bai samu tasgaro ba.

“Dalilin tsayuwata a nan shi ne bayyana fitowata takarar shugaban kasa da kwarin gwiwata, a karkashin inuwar jam’iyyar APC da aka kafa ta da mu.

“Aikin da ke gabanmu ba kokawa kan matsalolin kasarmu ba ne, aikinmu shi ne mu samu kwarin gwiwar kawo gyara a kasarmu ta zama giwar Afirka tare da kyautata  rayuwar ’yan Najeriya.

Oshiomhole ya kara da cewa: “Mukan bata lokaci kan sakamakon kurakurai da aka yi, maimakon gano tushensu da na abin da suke haifarwa.

“Yanzu da muke maganar matsalar tsaro da rashin aiki da talauci da rashin wutar lantarki, abin da ya kamata shi ne mu mayar da hankali kan yadda za a magance su.

“Abin da ya kamata a yi sabo shi ne mu daina korafe-korafe mu mayar da hankali wajen tattaunawa domin dawo da kyakkyawan fata,” inji shi.

Ya ce talauci da rashin tsaro da rashin aiki suna da alaka da juna, kuma, “Ba sai mutum ya zama farfesa kafin ya san talauci ba.”