✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

PDP ta dage zaben fidda dan takarar Gwamnan Edo

Jam’iyyar PDP ta dage zaben fitar da dan dakaranta a zaben Gwamnan Jihar Edo zuwa ranar 23 ga watan Yuni, sabanin ranakun 19 da 20…

Jam’iyyar PDP ta dage zaben fitar da dan dakaranta a zaben Gwamnan Jihar Edo zuwa ranar 23 ga watan Yuni, sabanin ranakun 19 da 20 ga watan Yunin da ta sanar a baya.

Sakataren Yada Labaran PDP na Kasa Kola Ologbondiyan ya ce Kwamitin Gudanarwar jam’iyyar na kasa ya yi haka ne saboda wasu abubuwan da suka taso na jam’iyyar.

Sanarwar ta bukaci ‘yan takara da magoya baya da masu fada a ji a jam’iyyar da su lura da sauyin sannan ta ba da tabbacin za a yi zaben a sabon ranar da aka sanar cikin ka’ida da kiyaye dokokin kairya na cutar coronavirus.

Wasu kwararan majiyoyi a hedikwatar jam’iyyar sun shaida wa wakilinmu a ranar Laraba cewa an dage zaben fitar da dan takarar ne domin ba wa Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki damar shigowa jam’iyyar ya yi takara.

Obaseki ya fice daga jam’iyyarsa ta APC ne bayan ta hana shi sake tsayawa takarar kujerarsa, sakamakon abin da wasu ke ganin zaman doya da manja tsakaninsa da tsohon maigidan kuma shugaban jam’iyyar na kasa Adams Oshiomhole ne ya haddasa. Daga bisani shi ma Oshiomholen kotu ta tabbatar da hukuncin da shi daga rike mukamin.

Kola Ologbondiyan ya tabbatar da cewa jam’iyyarsu na tattaunawa da Obaseki domin ganin ya sake dawo cikinta.

Hakan na zuwa ne yayin da wasu majiyoyi ke cewa tun bayan dakatar da Oshiomhole wasu gwamnonin APC na kai-komo domin ganin Obaseki ya dawo cikinta ya kuma yi takara.