✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

PDP ta jadadda dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo a Kano

PDP ta dakatar da shi bisa zargin yi mata zagon-kasa a zaben 2019.

Jam’iyyar PDP reshen Jihar Kano ta jadadda hukuncin kotu na dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo daga dukkan al’amuran da suka shafi jam’iyyar.

Shugaban jam’iyyar a jihar, Alhaji Shehu Wada Sagagi ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa da ya fitar a Kano.

“Awa biyu kafin zaben mambobin shiyya, PDP reshen Jihar Kano ta bada sanarwar dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo, bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-kasa a zaben 2019.

“Gabannin tunkarar zaben shugabannin PDP na Arewa maso Yamma, shugabannin PDP na dukkanin kananan hukumomi 44 na Jihar Kano sun hadu a ranar Laraba, inda suka amince kan dakatar da shi.

“Dakatarwar ta zo bayan samun shi da aka yi da hannu wajen hada baki da jam’iyyar APC a zaben 2019.

“Idan ba a manta ba mazabar Gwarzo ta fitar da sanarwar dakatarwa ga Sanata Bello Hayatu Gwarzo, wanda kuma shugabannin jam’iyya na jiha suka tabbatar da ita,” a cewarsa.

Sagagi ya ce jam’iyyar ta bi duk wasu matakai da ke cikin kudin tsarinta kafin dakatar da Sanata Gwarzo.

Kazalika, ya ce jam’iyyar ra dakatar da Hayatu Gwarzo wajen shiga ko damawa da shi a zaben shiyya da za a gudanar.

“Na tabbatar da cewa na samu dokar kotu wadda ta bada umarnin dakatar da Sanata Bello Hayatu Gwarzo shiga zaben shiyyar arewa maso yamma da za a yi.

“Don haka dole ne mu bi dokar kotu don shiga matsalar shari’a da dukkan matsalolin da ka je fa mu cikin damuwa kafin zaben 2023.

“Muna fatan zai fita daga cikin jerin ’yan takarar da ke neman mukami kakar yadda dokar kotu ta zayyana,” a cewar Sagagi.